Tinubu Ya Tura wa Atiku Saƙo bayan Cika Shekaru 80, Ya Tuna Halaccin da Ya Yi Masa

Tinubu Ya Tura wa Atiku Saƙo bayan Cika Shekaru 80, Ya Tuna Halaccin da Ya Yi Masa

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa
  • Tinubu ya bayyana cewa ya goyi bayan takarar Atiku ta shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Action Congress, duk da bambance-bambancen siyasa
  • Shugaban ya yabawa Atiku kan gudunmawarsa ga siyasar Najeriya, harkokin kasuwanci da ilimi, musamman kafa Jami'ar Amurka a Yola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, murnar cika shekaru 80 da haihuwa.

Tinubu ya tuna yadda ya goyi bayan burin Atiku na zama shugaban kasa a zaben 2007, yana mai cewa hakan ya samo asali ne daga imanin da yake da shi kan dimokuradiyya.

Hakan na cikin wata sanarwa da haɗiminsa na musamman, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Tinubu na fuskantar barazanar rasa kuri'u sama da miliyan 3 a 2027'

Tinubu ya yabawa Atiku bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban siyasar Najeriya, ilimi, kasuwanci da kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban ya bayyana cewa duk da bambancin jam'iyyun siyasa da ra'ayoyinsu kan al'amuran kasa, sun shafe shekaru suna mu'amala a siyasa tare da nuna kishin dimokuradiyya.

Ya ce goyon bayan da ya bai wa Atiku a zaben 2007 karkashin tsohuwar jam'iyyar Action Congress ya nuna yadda yake ganin ya kamata 'yan siyasa su samu 'yancin shiga harkokin dimokuradiyya da gabatar da nasu manufofin tafiyar da kasa.

Tinubu ya ce:

"Na goyi bayan Atiku ne saboda na yi imanin cewa dimokuradiyya tana bunkasa ne idan 'yan siyasa suna da 'yancin shiga harkokin siyasa, gabatar da wasu dabarun tafiyar da kasa da kuma bayar da gudunmawa kan yadda ya kamata a gudanar da mulki."

Haka kuma, shugaban ya sake jaddada bukatar gudanar da siyasa ba tare da gaba ko kiyayya ba, yana mai cewa ya kamata a rika sasanta bambance-bambance tsakanin abokan hamayyar siyasa.

Ya bayyana cewa dimokuradiyyar Najeriya tana amfana idan 'yan kasa suka ci gaba da mutunta tsarin dimokuradiyya, kokarin bunkasa kasa da bin doka, ba tare da la'akari da bambancin ra'ayoyin siyasa ba.

Kara karanta wannan

Shugaban FIFA ya leƙo ayyukan alherin Tinubu, ya faɗi ɓangaren da ya yi fice

Tinubu ya kuma yaba wa Atiku kan jarin da ya zuba wajen bunkasa kasuwanci da samar da ayyukan yi.

Musamman ya ambaci kafa Jami'ar American University of Nigeria da ke Yola, a jihar Adamawa, yana mai cewa jami'ar ta taimaka wajen fadada damar samun ingantaccen ilimi da bunkasa kwarewar matasa.

A cewarsa:

"Ko da yake ni da tsohon mataimakin shugaban kasa mun bi hanyoyi daban-daban a yanzu, kuma muna da sabanin ra'ayi kan al'amuran kasa, dole ne hadin kan Najeriya da zaman lafiyar dimokuradiyyarmu su kasance a gaba."

Shugaban ya yi wa Atiku fatan samun lafiya, karin karfin jiki da kuma tsawon shekaru domin ci gaba da yi wa Najeriya da bil'adama hidima.

Atiku Abubakar ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa 2007. Ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin fitattun 'yan siyasa a Najeriya, kuma shi ne dan takarar shugaban kasa na ADC a babban zaben 2027.

Karin bayani na yafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.