Jirgin Sojoji Ya Saki Bama Bamai a Zamfara, an Kashe Kachalla Gurgu
- Rundunar sojin Najeriya ta kai farmakin sama kan wata maboyar ‘yan ta’adda a Yankuzo da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara
- Rahotanni sun ce an kashe mayakan ‘yan ta’adda da dama yayin farmakin, yayin da wasu kuma suka samu raunuka masu muni sosai
- Daga cikin waɗanda aka ce an kashe akwai wani ɗan ta’adda mai suna Isiya Gurgu, wanda ake zargin yana kashe kashe a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara – Jami’an tsaron Najeriya ƙarƙashin Operation Fansan Yamma sun kai farmakin sama kan wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne a yankin Yankuzo, Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Majiyoyin yankin sun ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar 7 ga Satumban 2026, lokacin da jiragen yaƙin soji guda biyar suka gudanar da wani farmaki na haɗin gwiwa a yankin.

Source: Getty Images
Legit ta tattaro bayanai game da lamarin ne a wata sanarwa da mai sharhi kan lamuran tsaro Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
An kashe mayaka da dama
Majiyoyin sun bayyana cewa jiragen saman sojin sun kai hari kan wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne, inda aka samu rahoton kashe mayaka da dama.
Sai dai ba a iya tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka kashe ko suka jikkata ba a lokacin da ake tattara wannan rahoton.
An kashe Isiya Gurgu
Daga cikin waɗanda aka ruwaito an kashe akwai wani ɗan ta’adda mai suna Isiya Gurgu, wanda ake cewa yana daga cikin makusantan wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Musa Commander.
Ana danganta Musa Commander da ƙungiyar Ado Aleru, wadda ake zargi da ayyukan ta’addanci a wasu sassan jihar.
Majiyoyin sun kuma yi zargin cewa Musa Commander na da alaƙa da wasu al’ummomin da ‘yan ta’adda ke iko da su, ciki har da Tsamiya da wasu ƙauyuka da ke yankin.
A cewar majiyoyin, jami’an tsaron sun yi taka-tsantsan yayin gudanar da farmakin domin rage yiwuwar samun asarar rayukan fararen hula.
Rahoton ya ce farmakin ya fi mayar da hankali ne kan mutanen da aka gani ɗauke da makamai ko sanye da tufafin da suka yi kama da na sojoji.
An kuma ruwaito cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin ‘yan ta’adda ne sun samu raunuka yayin farmakin.

Source: Original
Yankuzo na daga cikin yankunan da ake zargin ƙungiyoyin ‘yan bindiga masu alaƙa da tsarin Ado Aleru suna amfani da su a matsayin mafaka.
An karawa sojoji albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da sabon tsarin albashi na ma’aikatan Rundunar Sojin Najeriya, inda Janar-janar za su samu kudi mai tsoka.
Takardar amincewar da Hukumar Albashi, Kuɗaɗen Shiga da Albashi ta Ƙasa ta fitar a ranar 3 ga Satumban 2026 ta ce sabon tsarin zai fara aiki daga 1 ga Satumban 2026.
Sabon tsarin ya ƙunshi sababbin adadin albashin shekara-shekara da za a yi amfani da su wajen lissafin fansho ga jami’an Sojojin Ƙasa, Ruwa da Sama.
Asali: Legit.ng

