Wanda Ya Tsira Ya Yi Magana, Ya Fadi Abin da Ya Jawo Mutuwar Mutane Fiye da 30 a Ofishin NSCDC
- Sababbin bayanai sun fito kan yadda wadanda ake zargi da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba suka rasa rayukansu a ofishin NSCDC
- Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ya ce waɗanda abin ya shafa sun yi ta neman iska saboda yadda aka cunkushe su kafin rasuwarsu
- Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, yayin da aka dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Minna, Niger — Sababbin bayanai sun bayyana kan rahoton mutuwar mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun hukumar tsaro da NSCDC a Jihar Neja.
Wani wanda ya tsira da rayuwarsa ya yi zargin cewa waɗanda suka mutu sun shaƙe ne bayan an cunkushe su a wani ɗaki da ba shi da isasshen iska.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce ɗan’uwansa ya ba da labarin abin da ya faru.
Ya bayyan cewa dan uwansa da y tsira ya fada masu cewa an zuba mutanen cikin wani ɗaki ba tare da isasshiyar iska ko fanka mai aiki ba.
A cewarsa, waɗanda abin ya shafa sun yi ta ihu da kuka suna neman iska, tare da yawan bugun wurin suna kiran a taimaka musu, amma jami’an da ke bakin aiki suka yi watsi da kukansu.
Yadda lamarin ya faru
Lamarin ya biyo bayan samamen tabbatar da doka da jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) suka gudanar a wasu sassan Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026.
Rahoton mutuwar mutanen ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis a yankin M.I. Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan
Tun ba a je ko'ina ba shirin hada kan 'yan adawa don tunkarar Tinubu ya gamu da cikas
Wannan sabon bayani ya ƙara jawo damuwa kan yanayin da mutanen suka mutu, yayin da Gwamnatin Tarayya ta riga ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
An dakatar da kwamandan NSCDC
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kuma bayar da umarnin dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, nan take, har sai an kammala binciken.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa babban abin da gwamnati ta fi ba da muhimmanci shi ne kare rayukan jama’a, kamar yadda Punch ta rahoto.
Ya buƙaci jama’a su kasance cikin natsuwa tare da bin doka, yana mai tabbatar musu cewa za a gudanar da bincike na gaskiya da gaskiya kan dukkan yanayin da ya haifar da lamarin.
Yadda mutum 33 suka mutu a ofishin NSCDC
A wani labarin, kun ji cewa mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula da Kare Muhalli ta Najeriya (NSCDC).
An ce Mutanen da suka mutu na daga cikin mutane 40 da aka tsare a sashen maza na ɗakin tsarewar NSCDC bayan kama su a wani samame.
Kwamandan NSCDC na Jihar Neja ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama waɗanda ake zargin ne a wani wurin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Asali: Legit.ng

