Shirye Shiryen Zaben 2027 Sun Kankama, INEC Ta Tura Muhimman Kayayyaki Jihohi
- INEC ta riga ta rarraba na’urorin BVAS guda 186,277, wanda ya kai kashi 75 zuwa 80 cikin ɗari na kayan aikin da take shirin amfani da su
- Hukumar ta ce Kano, Kaduna da Babban Birnin Tarayya Abuja na cikin wuraren da suka karɓi kayayyaki sosai
- INEC ta sayo ƙarin na’urorin BVAS guda 57,000, sannan ta rage yawan masu zaɓe da za a ɗora wa kowace na’ura daga 1,250 zuwa 850
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta riga ta rarraba kusan 75% zuwa 80% cikin 100% na na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS ga jihohi, gabanin babban zaɓen 2027.
Adadin na’urorin da aka riga aka rarraba ya kai guda 186,277, yayin da hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen tabbatar da gudanar da zaɓen cikin nasara.

Source: Facebook
Kwamishinan INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da jaridar The Punch a Abuja.
Ya ce mafi yawan jihohi sun karɓi kayan aikinsu, amma wasu ba su karɓi cikakken adadin da aka ware musu ba.
Mohammed Haruna ya ƙara da cewa za a kai dukkan sauran na’urorin da kayan zaɓe marasa muhimmanci ga jihohin kafin ƙarshen watan Nuwamba.
Kano da Kaduna sun karɓi kayan zaɓe
Da yake ƙarin bayani kan yadda rabon kayan ke gudana, Mohammed Haruna ya ce:
“Kusan 75% zuwa 80% cikin 100% na na’urorin BVAS an riga an kai su jihohi. Mafi yawan jihohi sun karɓe su, duk da cewa ba dukkansu suka karɓi cikakken adadin da aka ware musu ba.

Kara karanta wannan
Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki
“Wasu sun karɓi dukkan kayan, amma akwai wasu da har yanzu suke da ragowar na’urori kaɗan da za su karɓa."
Ya bayyana cewa Kano, Babban Birnin Tarayya Abuja da Kaduna na cikin wuraren da suka riga suka karɓi dukkan kayan zaɓe marasa muhimmanci da aka ware musu.
“Kusan dukkan jihohi sun karɓi kayansu. Amma daga cikin waɗanda suka kammala karɓa, na san Abuja, alal misali, da Kano da Kaduna ma.”
A makon da ya gabata, INEC ta bayyana cewa ta fara rarraba kayan zaɓe marasa muhimmanci ga wasu jihohi domin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
INEC ta sayo ƙarin na’urorin BVAS
A zaɓen 2023, INEC ta yi amfani da na’urorin BVAS guda 175,856 a rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin Najeriya.
Sai dai a watan Oktoba, shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya bayyana cewa INEC ta sayo ƙarin na’urorin BVAS guda 57,000 domin ƙarfafa amfani da fasaha a zaɓen 2027.
Bisa wannan ƙarin sayayya, jaridar ta ƙiyasta cewa hukumar za ta mallaki na’urorin BVAS guda 232,846 domin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Hukumar INEC ta ɗauki darasi, ta sauya tsarin da za ta yi amfani da shi a zaɓen 2027
Wannan na nuna ƙarin kusan 32.4% cikin 100% idan aka kwatanta da adadin na’urorin da aka yi amfani da su a zaɓen 2023.
INEC ta rage yawan masu zaɓe
Amupitan ya kuma bayyana cewa hukumar ta rage yawan masu zaɓe da za a iya haɗawa da na’urar BVAS guda ɗaya daga 1,250 zuwa 850.
Ya ce rumfunan zaɓe da ke da masu zaɓe sama da 850 za su samu na’urorin BVAS fiye da guda ɗaya domin gudanar da aikin tantance masu kaɗa ƙuri’a.
A zaɓen 2023, tsarin aikin da aka fi amfani da shi shi ne sanya na’urar BVAS guda ɗaya a kowace rumfar zaɓe.
Sabon tsarin na nufin wasu rumfunan zaɓe za su samu ƙarin na’urori, gwargwadon yawan masu zaɓen da aka yi wa rajista a cikinsu.

Source: Facebook
Gargadin INEC ga matasa kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi hannunka mai sanda ga matasa kan zaben shekarar 2027.
INEC ta bukaci matasan Najeriya da su ƙi shiga tashin hankalin zaɓe, amfani da siyasa wajen yaudarar jama’a, yaɗa ƙiyayya da kuma bayanan ƙarya gabanin babban zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
