Zaben 2027: Ma'aikata Za Su Huta, Dan Takara Ya Yi Alkawarin Biyan Mafi Karancin Albashin N500,000
- Omoyele Sowore ya yi alkawarin kafa mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa a 2027
- Ya kuma yi alkawarin samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba, da kuma tabbatar da cewa ilimi ya kasance kyauta kuma mai sauƙin samu ga kowa
- Ɗan takarar na AAC ya ce gwamnatinsa za ta gina gidaje miliyan ɗaya tare da sauya dokokin haya domin rage wahalar biyan kuɗin haya gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya yi alkawarin samar da mafi ƙarancin albashin rayuwa na N500,000 duk wata ga ma’aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.
Sowore, wanda ɗan gwagwarmaya ne, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin AAC za ta samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24, tare da tabbatar da samun ilimi kyauta kuma mai sauƙin samu a dukkan matakai.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya ki karbar tayin zama abokin takarar Atiku a ADC? An ji gaskiyar zance

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce manufofin AAC sun ta’allaka ne kan abin da ya kira “adalci na juyin-juya hali da daidaiton haƙƙoƙi”.
“Najeriya ƙasa ce mai matuƙar arziki”
Sowore ya ce Najeriya na da dimbin arziki, amma yawancin ’yan ƙasar ba sa cin moriyar arzikin saboda cin hanci da rashawa, rashin ƙwarewar shugabanci da kuma tsarin tattalin arziƙin da ke fifita wasu tsirarun ’yan siyasa da ’yan kasuwa.
“Manufarmu ita ce adalci na juyin-juya hali da daidaiton haƙƙoƙi. Najeriya ƙasa ce mai matuƙar arziki, amma an talauta ’yan Najeriya da gangan ta hanyar cin hanci da rashawa, rashin ƙwarewa da kuma tsarin tattalin arziƙin da aka tsara domin amfanar da ƙananan ’yan siyasa da ’yan kasuwa,” in ji shi.
Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan jin daɗin ma’aikata ta hanyar samar da mafi ƙarancin albashi na N500,000 duk wata.
Sowore ya ce ma’aikatan Najeriya ba za su ci gaba da karɓar abin da ya kira albashi na yunwa ba, yayin da sanatoci, gwamnoni da waɗanda aka naɗa mukamai ke karɓar miliyoyin naira a kowane wata.
Ya yi alkawarin wutar lantarki sa’o’i 24
Ɗan takarar AAC ya kuma yi alkawarin magance matsalolin wutar lantarki da ke addabar ƙasar, yana mai cewa gwamnatinsa za ta yi aiki domin samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
Ya ce babu wata ƙasa mai ƙoƙarin gina masana’antu mai ƙarfi da za ta iya dogaro da janareta har abada.
Sowore ya ƙara da cewa ilimi zai kasance kyauta kuma mai sauƙin samu a dukkan matakai, domin babu wani yaro ɗan Najeriya da ya kamata a hana shi ilimi saboda talaucin iyayensa.
Gidaje miliyan ɗaya da sauya dokokin haya
Dangane da gidaje da kiwon lafiya, Sowore ya ce gwamnatin AAC za ta gina gidajen jama’a masu matsakaicin farashi miliyan ɗaya.
Ya ce za a kuma sauya dokokin haya domin hana tilasta wa ma’aikata biyan kuɗin haya na shekara ɗaya ko biyu a take.
“Za mu fara aikin gina gidajen jama’a masu matsakaicin kuɗi miliyan ɗaya, tare da sauya dokokin haya domin kada a tilasta wa masu aiki biyan kuɗin haya na shekara ɗaya ko biyu a jere,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya
Game da kiwon lafiya, Sowore ya ce ya kamata kiwon lafiya ya zama haƙƙin kowane ɗan Najeriya, ba gata da aka tanada ga waɗanda ke da kuɗin zuwa ƙasashen waje neman magani ba.

Source: Twitter
Sowore zai dawo da tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na African Action Congress (AAC) a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.
Omoyele Sowere ya ce zai maido da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Asali: Legit.ng
