An Fitar da Bayanai kan Ganawa tsakanin Tinubu da Shugaban Faransa
- Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya karbi bakuncin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wani cin abincin dare na musamman a fadar Élysée da ke birnin Paris
- Ganawar shugabannin biyu ta sake jaddada dadaddiyar alakar Najeriya da Faransa da kuma kudurin kasashen na kara karfafa hadin gwiwa
- Tinubu ya isa Faransa ne a ranar Lahadi domin ci gaba da hutunsa na shekara-shekara na mako uku, bayan ya shafe bangaren farko na hutun a birnin Landan na Birtaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya karbi bakuncin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a wani cin abincin dare na musamman da suka yi a fadar Élysée da ke Paris ranar Alhamis da dare.
Ganawar ta kasance wani sabon mataki na hulda tsakanin shugabannin kasashen biyu yayin da Tinubu ke Faransa domin ci gaba da hutunsa na mako uku.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Bola Tinubu ya yi ne a wani sako da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 18 ga Satumban shekarar 2026.
Tinubu ya gana da Macron
Tinubu ya bayyana cewa ya ji dadin samun damar cin abincin dare na musamman tare da Macron a fadar shugaban Faransa.
Ya ce tattaunawar ta sake tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Faransa da kuma kudurin kasashen biyu na zurfafa hadin gwiwa.
Shugaban ya kuma gode wa Macron kan kyakkyawar tarbar da ya yi masa da kuma abokantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Abin da ganawar ta kunsa
A cewar bayanin da mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar, ganawar ta nuna dadaddiyar alakar Najeriya da Faransa.
Jaridar the Cable ta rahoto Onanuga ya ce shugabannin biyu sun sake jaddada kudurinsu na karfafa hadin gwiwar kasashen biyu da gina alaka mai amfani ga bangarorin biyu.

Source: Facebook
Tinubu na hutunsa a Faransa
Tinubu ya isa Faransa ranar Lahadi domin ci gaba da hutunsa na shekara na mako uku bayan ya shafe farkon lokacin hutun a Landan.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya fara hutun ne a ranar 30 ga Agustan 2026, inda aka bayyana cewa zai kasance hutun aiki yayin da yake Turai.
Rahotanni sun bayyana cewa an karbi shugaba Tinubu a Faransa ne ta hannun Jakadan Najeriya a kasar, Emmanuel Ayodele Oke.
Tinubu zai gyara dokar haraji
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Tarayya ta fara sake duba sababbin dokokin haraji na tsawon mako shida domin gano gibin da ke tattare da aiwatar da su da kuma magance illolin da suka bayyana.
Binciken zai kuma duba damuwar da bangaren masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki suka bayyana, musamman kan VAT, harajin ribar kadarori da biyan haraji fiye da sau daya.
Sababbin dokokin harajin sun fara aiki gaba daya ne a ranar 1 ga Janairu 2026, bayan da Tinubu ya sanya hannu kan dokokin guda hudu da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da su.
Asali: Legit.ng

