Hisbah Ta Cafke Shahararren Dan TikTok kan Yada Bidiyoyin Badala
- Hukumar Hisbah ta Kano ta kama Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International, kan yada bidiyoyin da ba su dace ba
- An ce wasu daga cikin bidiyonsa sun nuna yana rawa, rungume da mata, ɗaukar su, da kuma yin iyo ko wanka tare da su
- Hisbah ta ce za ta gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da gargaɗin matasa kan abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’a da addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani shahararren mai ƙirƙirar bidiyon TikTok, Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International
Hukumar Hisbah ta cafke Ukasha ne kan wasu bidiyonsa da suka nuna yana rungume da mata da yin wanka tare da su.

Source: TikTok
Jaridar Daily Trust ta ce mataimakin shugaban hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya tabbatar da kama Ukasha ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026.
Ya ce an kama matashin mai shekaru 27 ne bayan jami’an hukumar sun samu bayanan sirri cewa ya shigo jihar Kano.
An kama shi kan bidiyon TikTok
Aminuddeen ya bayyana cewa a halin yanzu Ukasha yana tsare a hannun hukumar, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A yayin binciken, Ukasha, wanda ɗan asalin Gusau ne a Jihar Zamfara kuma mazaunin Abuja, ya amince cewa ba zai iya tuna adadin bidiyon da ya shirya tare da mata ba.
Wasu daga cikin bidiyon sun nuna shi yana rawa, rungume da mata ko ɗaukar su, yayin da wasu ke nuna abubuwan da suka shafi iyo da kuma wanka.
Bidiyoyinsa sun yadu sosai
Mai TikTok ɗin ya bayyana cewa wasu daga cikin bidiyonsa sun samu wadanda suka kalla tsakanin mutane miliyan ɗaya zuwa uku.
Da aka tambaye shi yadda yake samun matan da yake bayyana tare da su a cikin bidiyon, Ukasha ya ce matan ne suke zuwa wurinsa saboda ya kasance mai ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a kafafen sada zumunta.
An kuma tambaye shi ko zai iya sanya ’yan’uwansa mata cikin irin waɗannan bidiyoyi, inda ya ce dukkan su suna da aure.
Ya ƙara da cewa mahaifiyarsa da wasu mutane da dama sun sha yi masa gargaɗi kan irin abubuwan da yake wallafawa.
Ya ce zai daina yada badala
Ukasha ya bayyana cewa tuni yake tunanin daina irin wannan nau’in abubuwan da yake samarwa, musamman yayin da yake shirin yin aure.
Ya nemi afuwa kan abubuwan da ya aikata, tare da yin alƙawarin cewa ba zai sake maimaita su ba.
Hisbah za ta gurfanar da shi a kotu
Dakta Mujahid Aminuddeen ya ce hukumar za ta gurfanar da Ukasha a gaban kotu bayan kammala bincikenta.
Ya kuma gargadi matasa da su guji amfani da TikTok wajen gudanar da ayyukan da suka saɓa wa ɗabi’a da kuma koyarwar addini.

Source: Original
Ciyaman ya shiga Hisbah
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Birniwa, Hon. Shehu Baba Birniwa, saboda shiga horon hukumar Hisbah da kansa.
Shehu Baba ya shiga horon ne bisa radin kansa, inda ya yi mako guda tare da jami’an Hisbah 2,449 da aka horas a jihar.
Asali: Legit.ng

