Wata Sabuwa: Tinubu Ya Dauko Sabon Gyara a Dokar Haraji ana Shirin 2027
- Gwamnatin Tarayya ta fara nazarin sababbin dokokin haraji na tsawon mako shida domin gano gibin da ke tattare da aiwatar da su
- Binciken zai kuma duba wasu illolin da suka bayyana tun bayan fara amfani da dokokin tare da la’akari da korafe-korafen ‘yan kasuwa
- Abubuwan da za a sake dubawa sun hada da iyakar VAT, yadda ake kula da ribar kadarori da kuma matsalar biyan haraji fiye da sau daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta fara nazarin sababbin dokokin haraji da aka fara aiwatarwa a Najeriya domin gano matsalolin da suka kunno kai da kuma gyara wuraren da ake bukatar karin bayani.
An ware wa kwamitin fasaha mako shida domin kammala aikin nazarin dokokin tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta aiwatar da su.

Source: Facebook
Abubuwan da za a sake dubawa
Daily Trust ta ce binciken zai mayar da hankali kan batutuwa da suka hada da iyakar harajin VAT, yadda ake lissafin harajin ribar kadarori da kuma matsalar biyan haraji fiye da sau daya.
Sababbin dokokin sun fara aiki gaba daya ne a ranar 1 ga Janairu 2026, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji guda hudu.
Dalilin sake duba dokokin
Yayin kaddamar da kwamitin fasaha kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji a Abuja jiya, Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya ce aiwatar da dokokin ya bayyana wuraren da ke bukatar karin bayani.
Punch ta wallafa cewa Oyedele ya ce gwajin dokar ya fara ne a lokacin da ta hadu da tattalin arziki, yayin da ‘yan kasuwa ke aiki da ita, jami’an gwamnati ke aiwatar da ita, masu zuba jari ke mayar da martani sannan jama’a ke fuskantar tasirinta.
Ya ce gwamnati ta koma daga yin manyan sauye-sauyen haraji zuwa ci gaba da inganta tsarin, yana mai cewa sake duba dokokin ba na nufin janye sauye-sauyen da aka yi a 2025 ba.

Source: Twitter
‘Yan kasuwa sun nuna damuwa
Kungiyoyin ‘yan kasuwa sun bayyana damuwa kan wasu tanade-tanaden sababbin dokokin haraji, musamman wadanda suka shafi kamfanoni.
A watan Yuni, kungiyoyin ‘yan kasuwa sun rubuta wasika ga Shugaba Tinubu, inda suka ce sabanin fahimtar wasu tanade-tanaden dokokin ya kawo cikas ga shigar da bayanan harajin kamfanoni a fadin Najeriya.
Kungiyoyin sun ce suna goyon bayan sauye-sauyen haraji da gwamnati ke yi, amma sun bukaci a samar da tsarin da zai ba su damar yin bayanan haraji daidai tare da biyan kudin da suka rataya a kansu.
Za a zare tallafin lantarki
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kawo karshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga shekarar 2027 domin samar da tsarin da zai kasance mai dorewa a bangaren wutar lantarki.
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa gwamnati za ta rika rage tallafin a hankali yayin da take kokarin biyan tsofaffin basussukan bangaren.
Tegbe ya ce kawo karshen tallafin ba zai hana masu amfani da wutar lantarki samun moriyar da suke samu ba, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin inganta samar da wutar lantarki da ayyukan bangaren.
Asali: Legit.ng

