Yan Bindiga Sun Mamaye Gidan Wani Kwamishina, Sun Bude Wuta ba Tare da Nuna Tausayi ba

Yan Bindiga Sun Mamaye Gidan Wani Kwamishina, Sun Bude Wuta ba Tare da Nuna Tausayi ba

  • Yan bindiga sun kai hari gidan Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari na jihar Imo, Rex Anunobi, a Owerri, babban birnin jihar da ke Kudu maso Gabas
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe wani sufeto na ’yan sanda da ke gadin gidan, lamarin da ya ja hankalin hukumomi
  • ’Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Owerri, jihar Imo - Wasu ’yan bindiga sun mamaye gidan wani kwamishina a Jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya, inda suka kashe wani sufeto na ’yan sanda da ke aikin gadi.

An ruwaito cewa sufeton yan sanda, Henry Effiong, yana gadin gidan Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari, Rex Anunobi, lokacin da maharan suka kai masa hari tare da kashe shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da dama sun mutu da suka gamu da bala'in da ya fi ƙarfinsu a daji

Jihar Imo.
Taswirar jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lamarin ya faru ne a safiyar Litinin da ta gabata a Owerri, babban birnin jihar Imo, kamar yadda jaridar Premium Times ta tattaro.

Majiyoyi sun ce ’yan bindigar sun fara kwace makaminsa, suka karɓi bindigar da yake ɗauke da ita da kuma wayoyinsa kafin su kashe shi.

’Yan sanda sun yi magana kan harin

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Mista Okoye, wanda mataimakin sufeton ’yan sanda ne, bai bayyana sunan sufeton da aka kashe ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce bayan samun rahoton lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Audu Bosso, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce manufar binciken ita ce gano yadda lamarin ya faru da kuma gano tare da cafke maharan.

Kakakin yan sandan ya ce:

“Bisa umarnin da aka bayar, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Jihar (SCID), tare da DPO na ’Yan Sandan sabuwar Owerri, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda aka gudanar da binciken da ya dace tare da kwashewa da adana muhimman kayayyakin da aka samu."

Kara karanta wannan

'Kashe kashe ya yi yawa': An taso gwamna a gaba sai ya bar kujerarsa

Yan sanda.
Wasu daga cikin jami'an hukumar yan sandan Najeriya da aka tura aikin zabe a Osun Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An kama waɗanda ake zargi

Mista Okoye ya sanar da cewa ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan sufeton.

“An kama waɗanda ake zargin, Olivia Patrick, namiji mai shekaru 31, da ThankGod Mourice, namiji mai shekaru 25, a wurin da lamarin ya faru jim kaɗan bayan an kai rahoton lamarin,” in ji shi.

Mai magana da yawun ’yan sandan ya ce an tura batun zuwa SCID domin ci gaba da bincike, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama sauran waɗanda ake zargin da suka tsere.

Yan sanda sun kashe kwamandan yan bindiga

Kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar kashe wani da ake zargi da jagorantar dabsr ‘yan ta’adda da ta addabi jama'a a jihar Imo.

Bayan tura jagoran zuwa lahira, dakarun ‘yan sanda sun kwato bindigar AK-47 da harsasai 56 a maboyar da ake zargin ‘yan kungiyar ke amfani da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262