Rigima Sabuwa: Amurka Ta Matsa kusa da Koriya, Kim Jong Un Ya Yi Gargadi
- Koriya ta Arewa ta yi gargadin cewa za ta kara mayar da martani ga atisayen sojin da Amurka da kawayenta ke gudanarwa a yankin Asiya da Pasifik
- Kanwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, Kim Yo Jong ta ce Pyongyang za ta ci gaba da karfafa karfin nukiliyarta na dakile barazana
- Kim Yo Jong ta kuma zargi Amurka da kasancewa babbar hanyar kara tabarbarewar zaman lafiya a yankin Koriya da sauran sassan kusa da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
North Korea – Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da kawayenta kan karin matakin soji, tana mai cewa za ta dauki matakan ramuwar gayya masu karfi idan ta ga barazana ga tsaro da ikonta.
Kim Yo Jong, wata babbar jami’a a jam’iyyar Workers’ Party kuma kanwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ta bayyana hakan ne ranar Juma’a.

Source: Getty Images
Kim Yo Jong ta soki Amurka
Anadolu Agency ta wallafa cewa Kim ta soki atisayen sojin ruwa na Pacific Vanguard 2026, wanda ya kunshi Amurka, Koriya ta Kudu, Japan da wasu kasashe a kusa da Guam.
Ta bayyana atisayen a matsayin wani atisayen yaki mai barazana, tana zargin Amurka da kokarin fadada tasirinta na soji ta hanyar kawancen kasashe a yankin Asiya da Pasifik.
Kim ta kuma soki karuwar hadin gwiwar soji tsakanin Amurka, Japan da Koriya ta Kudu, tana mai cewa Koriya ta Arewa ce babbar kasar da wannan hadin gwiwa ya fi mayar da hankali a kanta.
Kasar Koriya za ta kara shiri
Kim ta ce halin da ake ciki ya nuna bukatar Koriya ta Arewa ta kara daukar matakan martani, wadanda za su iya zama daidai da matakin da aka dauka a kanta ko kuma su fi shi tsauri.
Reuters ta wallafa cewa ta ce babu wani sauyi da zai faru a manufofin Pyongyang na ci gaba da karfafa karfin nukiliyarta na dakile barazana.
Kim ta yi gargadin cewa Koriya ta Arewa za ta iya amfani da dukkan hanyoyin da take da su idan aka yi barazana mai tsanani ga ikonta ko tsaronta.

Source: Getty Images
Maganar Koriya ta Kudu
Gargadin ya zo ne yayin da Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, ya ce ya kamata Seoul ta yi duk mai yiwuwa domin sake bude tattaunawa tsakanin Kim Jong Un da Shugaban Amurka Donald Trump.
Lee ya ce ba za a iya kawar da yiwuwar sake samun tattaunawar ba, yana mai cewa ya kamata Koriya ta Kudu ta yi iya kokarinta domin ganin an cimma hakan.
China ta yi magana da Iran
A wani labarin, kun ji cewa kasar China ta tuntubi Iran a sirrance domin ta nemi Tehran ta yi amfani da tasirinta wajen dakile mayakan Houthi na Yemen bayan Saudiyya ta nemi Beijing ta taimaka mata.
Lamarin ya biyo bayan ci gaban da Houthis suka samu cikin sauri a gabar tekun Red Sea da yankin mashigar Bab el-Mandeb, wanda ya kara fallasa jigilar man Saudiyya da harkokin sufuri a yankin.
China ta fito fili tana kira da a nuna kamewa da kai hare-hare, a koma tattaunawa tare da dawo da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa, yayin da ta tura sakon sirri ga Iran.
Asali: Legit.ng

