An Dakatar da Babban Jami'in Tsaro kan Mutuwar kusan Mutum 40
- Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, bayan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba
- Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa mutuwar mutanen
- Lamarin ya faru ne bayan an kama mutanen yayin samamen da rundunar ta gudanar a wasu sassan Jihar Neja tsakanin 15 da 16 ga Satumba 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) na Jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan nan take tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Gwamnoni, Malamai da manyan Arewa sun yi taro, sun yiwa Tinubu mubaya'a

Source: Twitter
Legit Hausa ta gano cewa wasu Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar da sanarwar ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Yadda aka kama mutanen
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin M.I. Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin Jihar Neja, a safiyar Alhamis.
A cewar sanarwar da mai ba ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Alao Babatunde, ya fitar ranar Juma’a, an kama mutanen ne yayin samamen da aka gudanar a wasu sassan jihar.
Samamen ya gudana ne tsakanin 15 da 16 ga Satumba 2026, a wani mataki na dakile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
An dakatar da kwamandan NSCDC
Tunji-Ojo ya ce lamarin abin takaici ne, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike yayin da aka dakatar kwamandan da lamarin ya faru a ƙarƙashin kulawarsa,
Ya ce gwamnatin tarayya ta sanya tsaron rayukan jama’a a matsayin babban abin da take ba muhimmanci.
Ministan ya kuma bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bin doka domin a gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci.

Source: Original
Adadin wadanda suka mutu
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 33 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne suka mutu yayin da suke tsare a hannun NSCDC.
Sai dai duk da haka, the Punch ta wallafa cewa rundunar NSCDC ba ta bayyana takamaiman adadin mutanen da suka mutu ba.
Bayanin jami'in NSCDC
A wani labarin, kun ji cewa jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce an kafa tawagar bincike ne a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Kwamandan Janar mai kula da Leken Asiri da Bincike.
An umurci tawagar da ta gudanar da cikakken bincike kan halin da mutanen suke ciki lokacin da aka kama su, lokacin da suka shafe a tsare da kuma yanayin wurin da aka tsare su.
Rahotanni sun nuna cewa binciken da za a yi zai kuma duba irin kulawar lafiya da aka ba mutanen tare da sauran abubuwan da suka shafi mutuwarsu
Asali: Legit.ng
