An Dauki Mummunan Mataki kan Malamin Addini bisa Zargin Batanci ga Iyayen Manzon Allah a Sokoto

An Dauki Mummunan Mataki kan Malamin Addini bisa Zargin Batanci ga Iyayen Manzon Allah a Sokoto

  • An caka wa Sheikh Musa Lukuwa wuka jim kaɗan bayan ya kammala jagorantar Sallar Juma’a a wani yanki na birnin Sokoto ranar Juma’a
  • Rahotanni sun ce harin ya biyo bayan zargin wasu kalaman batanci da aka danganta wa malamin game da iyayen Annabi Muhammad (SAW)
  • Wanda ake zargin ya kai harin ya mutu bayan wasu daga cikin mabiyan Sheikh Lukuwa sun far masa, yayin da malamin ke karɓar magani a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Fargaba da tashin hankali sun mamaye wasu sassan birnin Sokoto ranar Juma’a, bayan an caka wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa, wuka jim kaɗan bayan ya kammala Sallar Juma’a.

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan Sallar Juma’a, inda rahotanni suka ce ya samo asali ne daga zargin wasu kalaman batanci da aka danganta wa malamin game da iyayen Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

An farmaki Sheikh lukuwa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An caka wa Sheikh Lukuwa wuka

Jaridar Vanguard ta ce majiyoyi sun ce wani mutum ya tunkari Sheikh Lukuwa bayan an kammala sallar, inda ake zargin ya tambaye shi game da kalaman da ake ta cece-kuce a kansu.

Daga nan ne ake zargin mutumin ya caka wa malamin wuka, lamarin da ya jikkata shi.

Rahotanni sun ce an garzaya da Sheikh Lukuwa zuwa wani asibiti nan take, inda yake samun kulawar likitoci.

An kashe wanda ake zargin kai harin

Lamarin ya haifar da martani mai zafi daga wasu mabiyan malamin, waɗanda rahotanni suka ce sun far wa mutumin da ake zargin kai harin. Majiyoyi sun ce wasu daga cikin mabiyan sun kashe wanda ake zargin nan take.

Kisan ya ƙara jawo damuwa kan illar rikice-rikicen da suka shafi addini da kuma ɗaukar doka a hannu, musamman idan batun ya shafi zarge-zargen da za su iya tayar da hankalin jama’a.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da ma'aikatan lafiya ya gamu da hatsari dukkan mutanen ciki sun mutu

An yi kira ga bin doka

Lamarin ya sake haifar da kira ga a yi taka-tsantsan, a bar hukumomi su gudanar da bincike tare da bin hanyoyin doka wajen magance zarge-zargen da suka shafi batanci ko wasu batutuwan da ke da matuƙar muhimmanci ga addini.

Haka kuma, ya ƙara nuna buƙatar mutane su guji ɗaukar doka a hannunsu, ko da kuwa zargin da ake magana a kai yana da matuƙar ɗaukar hankali.

’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar wa Legit Hausa cewa lamarin ya faru.

"Eh tabbas lamarin ya auku. Matashin ya shiga masallacin da wuka a tare da shi wanda bayan Sallah ya sanya wa malamin ita a wuya. Mutane sun samu sun kwace shi inda aka kashe shi."
"Mun samu kiran gaggawa inda muka garzaya da matashin da malamin zuwa asibiti, an duba shi kuma har an sallame shi." In ji shi.

Kara karanta wannan

Ana zargin Bello Turji da kai mummunan hari a Sokoto da aka sace mutane 40

An yi yunkurin kashe Sheikh Sani Lukuwa
Sheikh Sani Lukuwa malamin addinin musulunci a Sokoto Hoto: Sani Hashidu
Source: Facebook

An yi zanga-zanga a sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutane sun fito kan tituna a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto kan matsalar rashin tsaro.

Masu zanga-zangar sun bayyana matuƙar damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng