Siyasar 2027 Ta Fara Daukar Zafi, Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Kamfen ADC

Siyasar 2027 Ta Fara Daukar Zafi, Yan Daba Sun Farmaki Tawagar Kamfen ADC

  • Ana zargin wasu ‘yan daba da kai hari kan tawagar kamfen ɗin ADC inda shugabannin jam’iyyar suka tsallake rijiya da baya
  • ADC ta ce an harbi wani magoya bayanta, Jerry Oliha, yayin da jam’iyyar ta zargi shugaban ƙaramar hukumar Igueben
  • Shugaban Igueben ya musanta hannu a lamarin, yayin da ‘yan sanda suka ce ba su samu rahoton hukuma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Edo - Rigimar siyasar 2027 a jihar Edo ta ɗauki sabon salo bayan wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari kan tawagar ADC.

Lamarin ya faru ne a yammacin Talata a ƙaramar hukumar Igueben, inda ake zargin maharan sun buɗe wa tawagar jam’iyyar wuta.

An kai hari kan masu kamfen ADC a Edo
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Wani jigo a jam’iyyar, tsohon ɗan takarar gwamna Kenneth Imasuangbon, da ɗan takarar sanatan Edo ta Tsakiya Herbert Okonofua sun tsira, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin hatsarin jirgi, an shiga sansanin sojojin Najeriya an kashe sama da 10

Wadanda suka tsira daga farmakin

Sauran shugabannin jam’iyyar da ke cikin ayarin ma sun tsira da ƙyar yayin da ake zargin ‘yan daban sun yi musu luguden wuta.

ADC ta zargi wasu masu biyayya ga jam’iyyar APC mai mulki da hannu a harin, tana mai cewa Endurance Azemegbe ne ya jagorance su.

Azemegbe shi ne shugaban ƙaramar hukumar Igueben, amma ya musanta hannu a harin, yana mai cewa bai ma kasance cikin Igueben ba.

Jam’iyyar ADC ta kuma ce wani ɗan goyon bayanta mai suna Jerry Oliha ya samu raunin harbin bindiga yayin harin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da shugabannin ADC ke gudanar da wasu ayyukan siyasa a yankin Igueben, kuma shi ne karo na uku.

A cewar jam’iyyar, an riga an kai irin wannan harin ta hanyar harbe-harbe a Ward 4 da Ward 5 na ƙaramar hukumar.

An kai hari kan masu kamfen ADC
Taswirar jihar Edo da aka kai wa ADC hari. Hoto: Legit.
Source: Original

Kalaman shugaba APC sun tada kura

Harin ya ƙara tayar da hankula game da tsananin siyasar Edo, musamman bayan wasu kalaman shugaban APC na jihar, Jarrett Tenebe.

Kara karanta wannan

A karshe, kotu ta ba da belin matasa da ke tsare kan sanya rigar 'Tinubu Must Go'

An ruwaito Tenebe yana barazanar amfani da AK-47 kan wasu abokan hamayya a ƙoƙarin jam’iyyar na samun kuri’u miliyan 2.5.

Sai dai ADC ta ce harin wani ɓangare ne na tsarin tashin hankali da ake zargin ana yi wa ‘yan adawa da wuraren jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce an samu irin waɗannan hare-hare a wasu ƙananan hukumomin Etsako ta Gabas, Owan ta Yamma da Owan ta Gabas.

Wanda ADC ke zargi game da hari a Edo

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ADC na jihar, Chris Ojeikere, ya fitar, jam’iyyar ta ce shugaban Igueben ya jagoranci maharan.

Sanarwar ta ce maharan sun kai wa tawagar Kenneth Imasuangbon da ɗan takarar sanatan Edo ta Tsakiya, Herbert Okonofua, hari.

ADC ta ce an harbi Jerry Oliha, matashin ɗan jam’iyyar daga Ward 6, a harabar fadar Enogie na Igueben.

Yan daba sun kai hari kan yan PDP

A baya, an ji cewa mutane uku sun jikkata, an lalata motoci yayin da wasu miyagu suka kai hari wurin tarukan tuntuba na PDP a jihar Cross River.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mahaifin dan takarar jam'iyyar ADC

Dan takarar gwamnan PDPna jihar Cross River ya ce ’yan bindiga sun kai hari kan tawagar magoya bayan jam’iyyar.

’Yan sanda sun ce sun tura jami’ai wuraren da lamarin ya faru, kuma yanzu komai yana karkashin kulawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.