Dubu Ta Cika: An Kama Wanda Ya Kashe Malamin Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

Dubu Ta Cika: An Kama Wanda Ya Kashe Malamin Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

  • Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama babban wanda ake zargi da kisan Malam Rilwanu Dauda a Karofin Madaki
  • An kashe malamin mai shekaru 46 ne bayan an kai masa hari tare da caka masa wuka a ranar 5 ga watan Yuli, 2026
  • ’Yan sanda sun ce suna ci gaba da farautar sauran waɗanda ake zargi da hannu a kisan domin doka ta yi aiki a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama babban wanda ake zargi da kisan wani malamin addinin Musulunci, Malam Rilwanu Dauda, a Karofin Madaki da ke cikin birnin Bauchi.

An ruwaito cewa Dauda, mai shekaru 46 kuma mazaunin Karofin Madaki, ya fuskanci hari tare da caka masa wuka daga wani Abdulrazak Sale, wanda aka fi sani da “Abba Sale Police."

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya rasa ransa bayan caka masa wuka a Jigawa kan N500 kacal

Dakarun yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yadda aka kashe malamin a Bauchi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Abba Sale Police, mai shekaru 24, wanda mazaunin yankin ne, tare da wasu ’yan ƙungiyarsa suka kashe malamin a ranar 5 ga Yuli, 2026.

An garzaya da wanda aka kashe zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.

An kama babban wanda ake zargi

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya bayyana a cikin wata sanarwa jiya cewa tun bayan faruwar lamarin, rundunar ta ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda ake zargi da suka tsere.

Haka zalika ya bayyana cewa rundunar yan sanda ta sanya sunayensu cikin jerin waɗanda take sa ido a kansu.

Ya ce a baya an danganta waɗanda ake zargin da wani kisan da aka yi a yankin wanda ake zargin yana da alaƙa da siyasa, kafin daga bisani su gudu su ɓoye.

Kara karanta wannan

Duk da gwamna ya sanya doka, an kashe malamin addini da wasu mutane sama da 20

Habib ya ce jami’an da ke aiki a sashen ‘A’ Division, Township, sun samu sahihin bayanan sirri daga wani mutumi, wanda ya taimaka wajen kama babban wanda ake zargi, Abdulrazak Sale Kundang, ranar Litinin.

Ya ce an kama shi ne daidai bayan shafe watanni uku da ake zargin ya aikata kisan, cewar rahoton Daily Post.

Ana farautar sauran wadanda ke zargi

Habib ya ƙara da cewa an ƙara tsaurara ƙoƙarin kamo sauran abokan aikata laifin da har yanzu suke gudu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewarsu da jajircewarsu.

Bauchi.
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya tabbatar wa mazauna jihar Bauchi cewa rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da farautar masu aikata laifuffuka a faɗin jihar, yana mai gargadin cewa babu wani mai laifi da zai samu mafaka a Bauchi.

Matar aure ta kashe kishiya a Bauchi

Kun ji cewa ana zargin wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, da kashe kishiyarta da tabarya a Tafawa Balewa Housing Estate da ke Bauchi.

‘Yan sandan Bauchi sun ce an kama wadda ake zargin tare da kwato tabaryan da ake zargin ta yi amfani da ita wajen aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262