Shugaban Amurka Ya Dora Laifin Abin da ke Faruwa a Faransa kan Addinin Musulunci

Shugaban Amurka Ya Dora Laifin Abin da ke Faruwa a Faransa kan Addinin Musulunci

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya dora laifin zanga-zangar ɗaliban Faransa kan kwararar baki da kuma addinin Musulunci
  • Ɗalibai sun toshe ƙofofin daruruwan makarantun sakandare a Faransa domin neman ingantattun yanayin karatu
  • Rahotanni sun nuna cewa kimanin masu zanga-zanga 250,000 ne suka fito kan titunan Faransa a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi yawan shigar baki da addinin Musulunci da haddasa zanga-zangar ɗalibai, wadda ke kara kamari a kasar Faransa.

Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya fitar, inda ya ce abin da ke faruwa a Faransa ya samo asali ne daga “yawan shigar baki kasar wanda ya wuce kima."

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana magana da manema labarai a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A rahoton da jaridar Vanguard ta wallafa, shugaban na Amurka ya kuma ce zanga-zangar ba ta da alaƙa da makarantu, yana mai zargin cewa Musulunci na son “ƙwace ikon wata ƙasa mai girma”.

Kara karanta wannan

Surutu ya ƙare, an yanke wa matashi hukunci kan taɓa martabar Annabi Muhammd SAW

Dalibai sun hana harkokin karatu

Tun daga ƙarshen watan Satumba, ɗaliban Faransa sun riƙa toshe ƙofofin ɗaruruwan makarantun sakandare a faɗin ƙasar domin neman gwamnati ta ainganta yanayin karatu.

Zanga-zangar dai ta haifar da wasu arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro a wasu wurare.

A ranar Talata, kimanin mutane 250,000 ne suka fito zanga-zanga a sassa daban-daban na Faransa.

Trump ya takura masu zuwa Amurka

Shugaba Trump da gwamnatinsa sun daɗe suna danganta wasu matsalolin zamantakewa a Turai da bakin da ke kwarara zuwa nahiyar.

Sun sha kira ga ƙasashen Turai da su rufe iyakokinsu, tare da maimaita ra’ayoyin jam’iyyun masu tsattsauran ra’ayi kan abin da suke kira durƙushewar wayewar Turai.

Manyan masu ra’ayi a ƙungiyar Make America Great Again (MAGA) ta Trump sun kuma yi amfani da zanga-zangar Faransa wajen ƙara jaddada batun baƙi gabanin zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na Amurka da za a gudanar a wata mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda fusatattun matasa suka so lakada wa Rarara duka kan tallata Tinubu

Masu sharhi masu goyon bayan MAGA sun sha wallafa bidiyoyin rikicin da ke faruwa a Faransa.

Shugaban Faransa.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron Hoto: Pablo Cuadra/Getty Image
Source: Getty Images

A ranar Litinin, Glenn Beck, wanda ke cikin masu goyon bayan Trump, ya ce tarzomar da ake gani a Faransa “gargaɗi ne karara ga sauran ƙasashen Yamma”.

Har yanzu dai Republican na nan kan bakarta game da batun baƙi da masu sauya jinsi, yayin da ake fargabar cewa rashin farin jinin Trump da yaƙin da Amurka ke yi da Iran na iya sa jam’iyyar ta rasa ikon Majalisar Dokokin Amurka.

Trump yabyi fatali da tayin Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi watsi da tayin Iran na bude mashigar Hormuz, yayin da ya nuna yiwuwar sabon harin bama-bamai.

Mashigar ruwan, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen samar da man.fetur ga duniya, ita ce cibiyar rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce za a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa idan Amurka ta cika sharuddan da suka gabatar mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262