An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko

An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko

Tsohon dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zamanin mulkin Soja, kuma tsohon Sarkin Gwandu, Mustapha Jokolo ya bayyana irin gudunmuwar da mashawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a sha’anin tsaro Sambo Dasuki ya baiwa Buhari a lokacin da ya zama shugaban kasa a mulkin Soja.

Buhari ya zama shugaban kasa ne a shekarar 1983 zuwa 1984, bayan wani juyin mulki da Sojoji suka yi ma gwamnatin shugaban kasa Usman Shehu Shagari, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Na fi kaunar mutanen da za su faɗa min gaskiya komai ɗacinta– Masari ga hadimansa

Jokolo ya bayyana kokarin da Sambo Dasuki ya yi ma Buhari ne cikin wata hira da jaridar The Sun, a wani raddi da yayi ma Muhammadu Bashar, mutumin da ya gaje shi a matsayin Sarkin Gwandu bayan an tumbuke Jokolo.

An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko
Buhari

Jokolo yace Dasuki, wanda bai wuce mukamin Manjo a wancan lokaci ya baiwa Buhari gudunmuwa ta kudi wajen samun nasarar juyin mulkin da yayi sanadin darewarsa mukamin shugaban kasa a karshen shekarar 1983.

“Ina jin zafin abin dake faruwa da Sambo Dasuki, musamman duba da rawar da ya taka wajen zaman Buhari shugaban kasa, kaga dai Sambo ne ya samar da duk kudaden da ake bukata wajen aiwatar da juyin mulkin, kuma Buhari bai bamu ko kwabo ba. Har daukan nauyin wasu Malamai yayi zuwa Makkah don su yi addu’ar samun nasarar juyin mulkin." Inji shi.

An bankado yadda Sambo Dasuki ya taimaka ma Buhari wajen darewa kujerar shugaban kasa a karo na farko
Jokolo

Hakazalika Kanal Abdulmuminu Jibrin ya musanta zargin da ake yin a cewa wai Sambo Dasuki ne ya jagoranci kama janar Buhari a lokacin da aka IBB yayi masa juyin mulki, inda yace babu kamshin gaskya cikin wannan magana: “Ni da Lawal Gwadabe da Jonh Madaki ne muka kama Buhari. Ni na jagorance su”

Daga karshe Jokolo yace shi da Lawal Gwadabe da Dasuki ne suka tafi har garin Jos inda suka yi ma Buharo karin jawabi game da shirye shiryen kifar da gwamnatin Shagari, wanda daga bisani Buhari ya fi kowa cin moriyar juyin mulkin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel