‘Yan Boko Haram Sun Yi Sabon Bidiyo da Ya Yi Maganar Batun Sulhu da Gwamnatin Tarayya

‘Yan Boko Haram Sun Yi Sabon Bidiyo da Ya Yi Maganar Batun Sulhu da Gwamnatin Tarayya

  • Kungiyar Boko Haram ta karyata batun tsagaita wuta da sunan an yi sulhu a boye da gwamnatin Najeriya
  • JAS ta bayyana cewa labarin yaudarar siyasa ce domin samun goyon bayan jama'a a lokacin zabe mai zuwa
  • Manyan shugabannin Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal Jihad ba su da masaniyar wannan maganar sulhun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Borno - Kungiyar Boko Haram ta karyata cewa ta yi sulhu da Gwamnatin Najeriya domin daina kai wa jama’a hare-hare.

Tsagin Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal Jihad (JAS) ya fito ya tabbatar da cewa babu wata yarjejeniya da suka yi.

Boko Haram
Motar yakin Boko Haram da sojoji suka kwace a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Yan Boko Haram sun fitar da bidiyo

Wani rahoton HumAngle ya ce ‘yan ta’addan sun fitar da bidiyo a ranar Lahadi, 13 ga Satumba 2026, suna karyata labarin sulhu.

‘Yan bangaren na Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati Wal Jihad sun ce ba a biya su kudi a asirce domin su daina kai hari ba.

Kara karanta wannan

Wasu malaman musulunci sun faɗa tarkon yan bindiga a hanyar dawowa daga taron APC

Wani sojan kungiyar ya yi magana da Larabci a bidiyon, daga baya ya yi Hausa, yana mai nanata cewa sam ba a sasanta da su ba.

Har sau uku wannan mutumi mai suna Mallam Abdulrahman ya fada cewa ba su yi sulhu a asirce da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ba.

Zancen sulhu da Boko Haram bai tabbata ba

A baya an yi ta yada cewa an shawo kan ‘yan ta’addan bayan biyan su kudi har suka amince su sako mutane 360 da suka kama kwanaki.

Rahoton da aka karyata ya ce gwamnati ta ba mayakan N5bn domin ganin tulin bayin Allah da aka dauke a garin Ngoshe sun dawo gida.

Abdulrahman ya yi magana a madadin Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’wati Wal Jihad, da ke karkashin jagorancin Mujahid Abu Umaima.

Mujahid Imam Abu Umaima shi ne shugaban kungiyar tun 2022, an fi sanin shi da Bakura Doro.

Boko Haram ta zargi gwamnati da yaudarar jama'a

‘Dan ta’addan ya ce kwanaki biyu da suka wuce su ma suka ji labarin sulhun a gidajen jaridu, kuma ya danganta lamarin da siyasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dawo da zancen zama mataimakin Atiku Abubakar a ADC kafin zabe

Sojan na kungiyar Boko Haram yake cewa ‘yan siyasa sun san lokacin zabensu ya zo, don haka an shiga kakar yaudar jama’a a kasar.

Yake cewa yaudara ta cika fagen siyasa don haka gwamnati ta zabi salo nan. Sai dai labarin sulhun ba daga wajen hukuma ya fito ba.

'Yan ta'adda ba su rufe kofar sasantawa ba

Duk da haka Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’wati Wal Jihad ta ce ita ba bakuwar sulhu ba ce, sai dai yanzu ba a yi wata yarjejeniya ba.

Wata majiya ta ce babu mamaki wasu tsirarun ‘yan kungiyar sun shiga yarjejeniya da gwamnati ne ba tare da tuntubar sauran ba.

Boko Haram
Sojojin da suka yi yakin Boko Haram a jihar Yobe Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Buhari ta tsaida sulhu da Boko Haram

An ji lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da tattaunawar sulhu da 'yan ta'addan Boko Haram saboda samun sabani cikinsu.

Shugaban kasa na lokacin ya tabbatar wa iyayen ɗaliban Chibok da aka sace cewa gwamnati ba za ta taɓa manta wa da 'ya'yansu ba, kuma za ta ceto su.

Buhari ya kuma buƙaci iyayen da kar su fitar da rai, yana mai cewa dawo da 'yan mata 100 da aka yi a baya shaida ce ta ƙoƙarin da gwamnatinsu ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng