Boko Haram sun shirya yin sulhu da gwamnati – Aisha Wakil

Boko Haram sun shirya yin sulhu da gwamnati – Aisha Wakil

Wannan lauyar da rundunar soja take nema ruwa a jallo, kuma makusanciya ga kungiyar Bokoharam Aisha Wakil ta bayyana cewa a shirye kungiyar take don shiga tattaunawar sulhu da gwamnati.

Boko Haram sun shirya yin sulhu da gwamnati – Aisha Wakil

Kungiyar Bokoharam da har yanzu suke kame da yan mata 219 da suka sace daga makaranatar yan mata ta garin Chibok sun aikata munanan ayyuka ta hanyar kashe jama’a bila adadin, tare da lalata dukiyoyin al’umma sun ce zasu amince da tattaunawar sulhu da gwamnatin tarayya.

Wannan batu ya fito ne daga bakin Aisha Wakil da ta kasance makusanciya na sosai da kungiyar a wata hira da tayi da jaridar ‘The Nation’.

“Tun da na dawo ina biye dasu, a yanzu sun yarda zasu zauna da gwamnati don su saki yan matan Chibok. In a goyon bayan yan matan Chibok da duk wanda aka kama. Amma yanzu haka yan Bokoharam sun shirya tattaunawa don samun lafiya. Wannan shi ne abin da suka fada min. ina tunanin wata kila su bada sanarwa ta shafin youtube nan bada dadewa ba”

Za’a iya tuna a ranar 14 ga watan agusta ne rundunar soja ta sanar da neman Aisha Wakil, Ahmad Salkida da Ahmed Umar Balori ruwa a jallo don binciken su. amma Aisha tayi tsokaci game da neman inda tace “ nine Aisha Wakil, ina sane da cewa rundunar soja na nema na tare da Salkida da Balori saboda alaka da yan Bokoharam. Abin ya bani dariya, sai yanzu suka yarda dani?”

“na san yan Bokoharama. Na dade ina kokarin ganin an samu zaman lafiya tun kafin a sace yan matan Chibok. Jami’an tsaron Najeriya sun sanni sarai, toh akan me zasu sanar da nema na?. mun sha zama tare da shugaban rundunar sojan kasa da mutanen sa. Na fada musu hanya mafi sauki shi ne a bari in kawo wasu manyan jagororin kungiyar don a tattauna, sais u gabatar da maganar sakin yan matan Chibok, amma suka ki, sun fi son cigaba da bin hanyar da suke bi.

“ina so in tabbatar ma yan Najeriya cewa bani da hannu a cikin wannan tirka tirka, sa’annan ina so su san cewa muna tattaunawa da rundunar sojan kasar nan, kuma sun san inda zasu neme ni, hakan yasa nayi mamakin yadda suka sanar da neman nawa a kafafen yada labarai, har da kiran sunan mijina.

“wannan ya sanya dangina shiga rudani da rikirkicewa, na san bai kamata ayi min haka ba. Idan ma basu gamsu da hanyoyin da na kawo na kawo karshen yaki da Bokoharam ba, toh ai bai kamata su bata min suna ba, Nagode”

Da wannan zancen da Aisha Wakil tayi da kuma zance da shugaba Buhari yayi a kasar Kenya, da alama an kusa kammala yaki da yan Bokoharam.

Shugaba Buhari yace ‘nayi wasu yan maganganu dangane da yan matan Chibok, amma sai aka siyasantar da maganan. Abin da muka ce shi ne, gwamnatin mu ta shirya tattaunawa da asalin shuwagabannin kungiyar Bokoharam. Idan ba za suyi magana da mu ba, toh su zabi wata kungiya mai zaman kanta, su tabbatar musu suna rike da yan matan, sa’annan su tabbatar da zasu sake su tare da tabbatar da suna bukatan a sako musu shuwagabanninsu.

“idan suka yi haka, toh Najeriya a shirye take ta saurare su”

A wani labarin kuma, an hana yan kungiyar dake karajin dawo da yan matan Chibok wato ‘’Bring back our Girls” daga shiga fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng