Ana cikin Jimami, Kasar Turkiyya Ta Aiko Sako Najeriya kan Hatsarin Jirgin Sojoji

Ana cikin Jimami, Kasar Turkiyya Ta Aiko Sako Najeriya kan Hatsarin Jirgin Sojoji

  • Gwamnatin Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga Najeriya kan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da ya yi sanadin mutuwar mutane
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce ta yi matuƙar baƙin ciki kan asarar rayuka 32 da hatsarin jirgin sojin ya jawo
  • Jirgin mai lambar wutsiya NGR 931 ya ɓace daga na’urar kila da zirga-zirgan jiragen aama yayin da yake kan hanyarsa daga Benin City zuwa Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamnatin kasar Turkiyya ta shiga jerin masu alhinin hatsarin jirgin rundunar sojojin saman Najeriya, wanda ya jawo asarar rayukan fararen hula da dakaru 32.

Kasar Turkiyya ta aiko da saƙon ta’aziyya ga Najeriya kan hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da ya yi sanadin mutuwar mutane a Jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba

Tinubu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu tare da takwaransa na kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan Hoto: Mustafa Kamaci/Anadolu
Source: Getty Images

Turkiyya ta aiko sakon ta'aziyya ga Najeriya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana ta’aziyyar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, 2026, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ma’aikatar ta ce ta yi matuƙar baƙin ciki kan asarar rayukan da hatsarin jirgin sojin ya haddasa a Jihar Ondo ranar 5 ga Oktoba, 2026, lamarin ya jefa iyalai da dama cikin jimami.

“Mun miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hatsari da kuma al’ummar Najeriya,” in ji ma’aikatar.

Yadda jirgin ya bace a hanyar Legas

An ruwaito cewa jirgin mai lambar aiki ta NGR 931 yana gudanar da aiki ne kamar yadda ya saba daga Benin City a Jihar Edo zuwa Legas, kafin ya ɓace.

Bayanai sun nuna cewa jirgin ya bace kuma sanrwarsa ta katse da misalin ƙarfe 9:13 na safe ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi maganar hatsarin jirgin saman sojoji a Ondo, ya bayar da umarni

Daga bisani jirgin ya yi hatsari kusa da sansanin Sojojin Ruwa na Igbokoda da ke Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.

Jirgin NAF.
Jirgin helikwafta na rundunar sojin saman Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigAirForce
Source: Getty Images

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce mutane 32 ne ke cikin jirgin, waɗanda suka haɗa da ma’aikatan jirgin biyar da fasinjoji 25.

Ejodame ya tabbatar da cewa babu wanda ya tsira da ransa daga cikin wadanda ke cikin jirgin saman.

Saƙon ta’aziyyar Turkiyya ya shiga jerin sauran saƙonnin nuna goyon baya da haɗin kai da Najeriya ke samu bayan wannan mummunan lamari, yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin gano abubuwan da suka haddasa hatsarin.

Janar Musa ya mika sakon ta'aziyya

Kun ji cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana matuƙar jimami kan hatsarin jirgin NAF ATR 42 da ya yi sanadin mutuwar mutane 32.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare: NAF ta fitar da cikakken bayani kan jirgin saman da ya yi hatsari a Najeriya

Musa ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin sojin Najeriya da iyalan waɗanda suka rasu.

Ministan ya ce an bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka haifar da hatsarin domin gano musabbabinsa,

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262