Mun dakatar da sulhu da Boko Haram - kalaman shugaba Buhari

Mun dakatar da sulhu da Boko Haram - kalaman shugaba Buhari

- Suhu da Boko Haram ya faro ne tun bayan da "yardaduwa ya murkushe shu

- Shugaban kasan yace matsalar ta biyo baya ne sanadiyyar rashin magana daya daga yan'ta'addan

- Daidaitawa tsakaninmu da Boko Haram ta tsaya- Buhari

Mun dakatar da sulhu da Boko Haram - kalaman shugaba Buhari
Mun dakatar da sulhu da Boko Haram - kalaman shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a ranar juma'a cewa Daidaitawa tsakanin Gwamnatin tarayya da yan'ta'addan Boko Haram domin sakin sauran yam'matan makarantar Chibok ya samu ci bayan da ba'ayi zato ba.

A wani zance na mataimaki na musamman na yada labarai ga shugaban kasar, malam Garba Shehu yace Buharin yana taya Gwamnatin jihar Borno, iyayen yam'matan da kuma jama'ar Najeriya na tuna tsautsayin da ya faru, da addu'ar cewa taron da za'ayi a ranar asabar a makarantar yam'matan zai tafi yanda ake so.

Buhari ya tabbatar ma da iyayen yam'matan da aka sace a makarantar yam'mata ta gwamnati da ke chibok, jihar Borno a ranar 14 ga watan Afirilu, 2014 cewa "Baza'a taba mantawa da ya'yansu mata ba, ko kuma a barsu, duk da shekaru hudun da akayi da sace su"

"Munsan ba wannan labarin iyayen suke son ji ba bayan shekaru hudu da sukayi suna jira, amma muna so mu kwatanta gaskiya daidai gwargwado."

"Duk da haka, Gwamnatin nan bazata taba gajiya ba. Zamu cigaba da jajircewa kuma muna rokon iyayen da kada su cire rai. Kada su cire ran ganin dawowar yam'matan mu gida. Kada ku fitar da ran cewa Gwamnati zata cika muku alkawarin dawo muku da yaranku"

"Kada ku taba tsammanin mun manta da yaranku ko mun dau yancinsu mara amfani" inji shugaban kasar.

DUBA WANNAN: Daren Israi da Mi'iraji

Yayi kira ga iyayen yaran da kada su fitar da ran dawowar yaransu, dawowar yam'matan 100 daga cikin wadanda aka sace ta hannun Gwamnatin tarayya kadai ya isa tabbatar musu da kokarin Gwamnatin "in da rai, da rabo"

"Munsan da cewa mun daukar lokaci kafin mu dawo da sauran yam'matan gida amma muna iya bakin kokarin mu don ganin mun kwato su daga yan'ta'addan " Buharin yace.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel