Atiku Ya Ragargaji Tinubu yayin da Farashin Fetur Ya Kusa kai N1,500

Atiku Ya Ragargaji Tinubu yayin da Farashin Fetur Ya Kusa kai N1,500

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda farashin man fetur ya kai N1,470 kan kowace lita
  • Atiku ya ce farashin danyen mai a yanzu ya kai $102.52 kan kowace ganga, amma 'yan Najeriya na biyan kudin mai fiye da lokacin da danyen mai ya kai $147 a 2008
  • Dan takarar shugaban kasa na ADC ya kuma bukaci gwamnati ta bayyana yadda aka tafiyar da kudin da aka samu bayan cire tallafin man fetur tun daga 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan karin farashin man fetur a Najeriya.

Atiku ya ce 'yan Najeriya yanzu suna biyan N1,470 kan kowace lita, duk da cewa farashin danyen mai a kasuwannin duniya bai kai matsayin da ya taba kaiwa a shekarar 2008 ba.

Kara karanta wannan

An fara rade radin kulla sabuwar hadaka domin kifar da Tinubu a 2027

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Bola Tinubu a gefen hagu, Atiku Abubakar a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Paul Ibe
Source: Facebook

Maganar Atiku Abubakar kan fetur

Vanguard ta wallafa cewa a wata sanarwa da hadiminsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce danyen mai a yanzu yana kan $102.52 kan kowace ganga.

Ya ce a 2008, lokacin da danyen mai ya kai kusan $147 kan kowace ganga, farashin man fetur ya kasance N65 kan kowace lita a zamanin marigayi Shugaba Umar Musa Yar'Adua.

Atiku ya ce bambancin ya nuna cewa gwamnatin wancan lokacin ta fahimci cewa manufofin tattalin arziki ya kamata su kare jin dadin al'umma.

'Ina kudin da aka samu?'

Atiku ya ce bai dace gwamnati ta ci gaba da kara wa 'yan Najeriya nauyin rayuwa bayan cire tallafin man fetur ba tare da bayyana yadda aka tafiyar da kudin da aka samu ba.

Ya tuna cewa an shaida wa 'yan Najeriya cewa cire tallafin zai samar da karin kudi ga bangarorin ilimi, lafiya, abubuwan more rayuwa da sauran muhimman ayyuka.

Kara karanta wannan

Yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta, farashin mai ya tashi a Najeriya

Sai dai ya ce bayan kusan shekaru uku da rabi, har yanzu akwai tambayoyi kan inda kudin da aka samu daga wannan mataki suka tafi.

Atiku ya ce farashin mai na N1,470 ba wai kawai yana shafar masu sayen man fetur ba ne, domin yana kara kudin sufuri, abinci, zuwa makaranta, noma, masana'antu da sauran abubuwan da 'yan Najeriya ke saya.

Atiku na so a binciki kudin FAAC

Atiku ya ce bayanan Asusun Tarayya na FAAC da kansu sun isa a kara sanya ido kan yadda ake tafiyar da kudin kasar.

Ya bayar da misali da watan Yunin 2025, inda ya ce kudin da aka tara a asusun tarayya sun kai N4.232trn, amma N1.818trn ne kawai aka raba ga hukumomin gwamnati.

Gidan mai a Najeriya
Mutane na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta rahoto ya ce an ware wasu makudan kudi a matsayin kudin karbar haraji, canja wuri, tallafi, mayar da kudi da kuma ajiyar kudi.

Dangote ya kara kudin mai

A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote ta ci gaba da kara farashin man fetur duk da cewa farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya kasance kasa da matakin da aka samu a lokacin karin farashin mai na baya.

Kara karanta wannan

Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Sabon karin ya kai farashin man fetur zuwa N1,350 kan kowace lita, wanda shi ne mafi girman farashin da matatar ta taba sanarwa tun bayan fara aiki a 2024.

Sabon farashin ya fara aiki ne ranar Asabar, inda ya karu da N85 daga N1,265 kan kowace lita, yayin da danyen man Brent ke kan kusan $104 kan kowace ganga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng