Dangote: Yadda aka Kara Kudin Fetur Sau 4 a Najeriya a Kasa da Wata 1

Dangote: Yadda aka Kara Kudin Fetur Sau 4 a Najeriya a Kasa da Wata 1

  • Matatar Dangote ta sake ƙara farashin fetur daga N1,265 zuwa N1,350 kan lita, wanda ya zama mafi girman farashin da ya taɓa sanya wa man a tashar lodinsa
  • Sabon ƙarin ya zo ne duk da cewa farashin ɗanyen mai na Brent da ake amfani da shi wajen auna farashin gangar mai a duniya yana kusan dala 104
  • A cikin kwanaki 22 kacal, Dangote ya ƙara farashin fetur sau 4, inda farashin ya tashi daga N,165 zuwa N1,350, wato ƙarin Naira 185 ko kashi 15.9 cikin 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Matar Dangote ta sake ƙara farashin fetur, inda farashin man a tashar lodinsa ya tashi zuwa N1,350 a kan kowace lita.

Sabon farashin ya fara aiki ne ranar Asabar, bayan kamfanin ya ƙara N85 daga farashin N1,265 kan lita.

Kara karanta wannan

Yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta, farashin mai ya tashi a Najeriya

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote da matatar shi da ke Legas. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Punch ta ruwaito cewa wannan shi ne mafi girman farashin fetur da matatar Dangote ta taɓa sanarwa tun bayan fara aiki a shekarar 2024.

Dangote ya ƙara farashin mai

Rahotannin sun bayyana cewa sabon ƙarin farashin mai da Dangote ya yi ya kasance na huɗu da matatar ta yi tun ranar 21 ga Agusta.

Vanguard ta wallafa cewa a ranar 21 ga Agusta, kamfanin ya ƙara farashin daga N1,165 zuwa N1,185 kan lita.

Bayan kwana biyar, ya sake ƙara N15 zuwa N1,200, kafin ya ƙara wasu N65 a ranar 29 ga Agusta zuwa N1,265.

A ranar Asabar kuma, an sake ƙara N85, wanda ya kai farashin zuwa N1,350 kan lita.

Jimillar ƙarin ya kai Naira 185, wanda yake wakiltar ƙarin kashi 15.9 cikin 100 cikin ƙasa da wata guda.

Batun farashin ɗanyen mai

An yi sabon ƙarin ne yayin da danyen man Brent ya kai kusan dala 104, bayan tashin farashin mai a duniya sakamakon matsalolin samar da mai da suka shafi rikicin Amurka da Iran.

Kara karanta wannan

Bayan korafi kan tallafi, Dangote ya kara farashin litar man fetur a Najeriya

Wannan ya jawo hankali ne saboda farashin ɗanyen mai a yanzu yana ƙasa da matakin da ya kai a lokacin tashin farashin mai na baya.

Mutane a gidajen mai a Najeriya
Ana sakawa mota fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bincike ya nuna cewa lokacin da Brent ya haura dala 115 kan ganga a baya, farashin fetur na Dangote a tashar lodinsa bai kai Naira 1,300 ba.

Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce Dangote na mayar da martani ne ga farashin mai a kasuwannin duniya.

Ukadike ya yi gargadin cewa farashin fetur na iya kai N2,000 kan lita idan Gwamnatin Tarayya ba ta ɗauki matakin dakile tashin farashin ba.

Atiku ya yi wa Dangote martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce gargadin matatar Dangote kan tilasta wa matatun mai sayar da fetur a farashin da zai jefa su cikin asara yana kan hanya.

Atiku ya zargi gwamnatin tarayya da karkatar da tsarin da ya gabatar domin ɓata masa suna, yana mai cewa bai taɓa son a tilasta wa matatar mai zaman kanta sayar da fetur ƙasa da kuɗin da ta kashe wajen samar da shi ba.

Ya ce tsarin nasa na tallafin samar da mai an tsara shi ne domin kauce wa irin wannan yanayi, tare da kare masu zuba jari da tabbatar da samun mai a farashi mai sauƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng