Syria: Mutane Sun Barke da Zanga Zanga kan Tsadar Man Fetur da Gas
- Rahoto ya nuna cewa birane da dama a kasar Siriya sun barke da zanga-zanga biyo bayan karin farashin fetur da gidan mai na gwamnati ya yi
- Masu zanga-zanga sun rufe babbar hanyar kasar tare da kona tayoyi bayan gwamnati ta kara farashin man dizal da kashi 40 a fadin kasar
- Gwamnatin kasar Syria ta alakanta karin kudin man da tsada da kuma karkatar da albarkatu wajen gyara babbar cibiyar tace mai ta Baniyas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Damascus – Jama'a da dama sun fito tituna a birane daban-daban na ƙasar Siriya domin nuna adawa da matakin gwamnatin ƙasar na ƙara farashin man fetur da dizal.
Matasa masu nuna fushin su sun rufe babbar hanyar ƙasar ta tsawon sa'o'i da dama tare da ƙona tayoyi a kan tituna domin neman gwamnati ta janye matakin.

Source: Getty Images
Tashar Al Jazeera ta ruwaito cewa an sami gudanar da irin waɗannan zanga-zangar a biranen Hama, Khan Sheikhoun, da kuma Maarat al-Numan, inda hakan ya haifar da zafafan muhawara a shafukan sada zumunta.
Matakin da gwamnati ta ɗauka
A ranar Lahadi ne gwamnatin ƙasar ta samamin ƙarin farashin dizal da kashi 40 cikin 100, yayin da aka ƙara farashin fetur da kashi 28 cikin 100.
Rahoton Arab News ya nuna cewa gwamnatin ta bayyana cewa:
"Wannan ƙarin kudin mai mataki ne na wucin gadi wanda hauhawar farashin danyan mai a kasuwar duniya ya haifar, tare da buƙatar gyara babbar cibiyar tace mai ta Baniyas domin haɗa ƙarfin sarrafata daga ganga 80,000 zuwa 130,000 a kullum."
Ana karancin man fetur a Siriya
Ministan Makamashi na Siriya, Mohammed al-Bashir, ya bayyana cewa a yanzu haka ƙasar tana hako gangar mai 102,000 ne kawai a kullum, alhali tana buƙatar ganga 325,000 domin amfanin gida.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasar (SANA) ta ruwaito cewa Ma'aikatar Makamashi ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da duba farashin idan kasuwar duniya ta canza.

Source: Getty Images
Hakan ya zo ne yayin da gwamnatin kasar ta ce tana ƙoƙarin faɗada harkar tace mai don sake gina tattalin arzikin ƙasar bayan shekaru 14 na yaƙi.
An kara kudin mai a Najeriya
A wani labarin daban, mun ruwaito cewa matatar man Dangote ta ci gaba da ƙara farashin fetur ɗinta duk da cewa farashin danyan mai a kasuwar duniya ya yi ƙasa idan aka kwatanta da wanda aka samu a watan Maris.
A halin yanzu, matatar ta ƙara farashin fetur din zuwa N1,350 a kowace lita daga N1,265, wanda shi ne mafi tsada tun bayan fara aiki da matatar a shekarar 2024.
Irin wannan ƙari ya fito ne a daidai lokacin da farashin danyan mai na Brent ke kan dalar Amurka 104 a ko wace ganga, sakamakon tashin hankalin da ke tsakanin Amurka da Iran wanda ya shafi harkar kasuwancin mai a duniya.
Asali: Legit.ng

