An Lissafa Tiriliyoyin Kudin da Za a Kashe idan Aka Maido Tallafin Man Fetur

An Lissafa Tiriliyoyin Kudin da Za a Kashe idan Aka Maido Tallafin Man Fetur

  • Yanke tallafin mai a 2023 ya tsananta rayuwar 'yan kasa ta hanyar hauhawar farashin kayan abinci da sufuri
  • Dawo da tsarin zai sa gwamnati ta rika kashe kudi Naira biliyan 52.5 a kowace rana, kusan N20tr kenan a shekara
  • Masana tattali sun kawo shawarar a rage radadin matsin rayuwa maimakon maida tsohon tsarin tallafin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Masana suna ganin dawo da tallafin da ake biya na man fetur zai ci wa Najeriya Naira tiriliyan 20 a kowace shekara.

Ban da kudin da gwamnati za ta batar, CPPE ta ce kokarin maido da tallafin fetur zai jefa kasar cikin matsin tattali da kuma bashi.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da wani yana zuba fetur a gidan mai Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maido tallafin fetur na nufin N20tr a shekara

Cibiyar CPPE ta yi matsaya cewa illolin dawo da tsarin tallafin mai sun zarce moriyar da za a ci na wani gajeran lokaci in ji jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Dangote ya fara sayar da hannun jarin matatar shi

Shugaban CPPE, Dr. Muda Yusuf ya ce idan za a samar da tallafi domin saida lita a kan N1050, gwamnati za ta ci kusan N20tr a shekara.

Ya yi lissafi da cewa a kaddara ana shan litoci miliyan 50 a kowace rana. Hakan yana nufin a kullum za a kashe N52bn sai N1.57tr a wata.

Idan aka hada wannan adadi, za a ga cewa tallafin zai ci wa gwamnati N19.16tr duk shekara.

Wasu abubuwa game da lissafin kudin tallafin mai

Ba dole lissafin ya tabbata haka ba don wasu alkaluman kamar farashin gangar mai, darajar dala da kudin dako da sauran za su yi tasiri.

Haka zalika idan aka maido tallafin, yawan man da ake sha zai karu, Muda Yusuf yana ganin za a dawo da fasa kauri zuwa kasashe.

Leadership ta rahoto shi yana cewa idan aka bar gwamnati da dawainiyar N20tr na tallafi, dole za ta dogara sosai da cin bashin kudi.

Kara karanta wannan

Daukar doka hannu: Matasa sun kashe tsoho dan shekara 80 bisa zargin aikata maita

Biyan tallafi zai hana yin ayyukan cigaba

A maimakon gwamnati ta ji da muhimman ayyuka, za ta yi ta kashe kudinta domin saukaka wa al’umma wajen sayen man fetur.

Hakan zai taba kudin da ake kashe wa a samar da abubuwan more rayuwa, harkar ilmi, kiwon lafiya, tsaro, da noma da dai sauransu.

N47tr aka ware wa kasafin kudin 2025, Dr. Yusuf ya ce karin N20tr a kan wannan yana nufin sama da 40% na abin da za a kashe.

Abubuwan da ya kamata a yi maimakon tallafi

A madadin dawo da tallafin, masanin ya kawo shawarwarin yadda za a taimaki rayuwar talaka.

An ba da shawarar matakai da suka hada da samar da zirga-zirgar jama’a mai saukin kudi da inganta jigilar kayayyaki ta jirgin kasa.

Haka zalika an nemi a inganta samar da wutar lantarki tare da samar da CNG da makamashin hasken rana a matsayin madadin shi.

Akwai maganar tallafa wa noma da bada tallafi kai tsaye ga gidaje masu fama da talauci da kuma inganta harkokin kiwon lafiya da ilimi.

Kara karanta wannan

Yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta, farashin mai ya tashi a Najeriya

Cikin shawarwarin akwai rage kudin yin kanana da matsakaitan sana’o’i da kamfanoni (MSMEs); da kuma dage wa wajen tace mai a gida.

Fetur
Wani gidan mai na NNPC a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Atiku Abubakar zai maido tallafin fetur

An ji Atiku Abubakar da yake neman zama shugaban kasa a 2027 ya dage cewa gwamnatinsa za ta dawo da tsarin tallafin mai a Najeriya.

Ban da Atiku akwai masu neman zama shugaban kasa a jam'iyyun Accord da AAC da sun sha alwashin karya farashin fetur idan aka zabe su.

Gwamnatin Bola Tinubu mai-ci da kuma wasu ‘yan takaran irin Peter Obi suna adawa da wannan kokari na ganin man fetur ya yi araha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng