Cikin Awa 1 da Bude Saida Hannun Jari, Matatar Dangote Ta Samu Dala miliyan 7

Cikin Awa 1 da Bude Saida Hannun Jari, Matatar Dangote Ta Samu Dala miliyan 7

  • Masu zuba jari sun saye hannun jarin da darajarsu ta haura dala miliyan 7 (Naira biliyan 10 a matatar Dangote
  • Bayanai sun tabbatar da jim kaɗan bayan Matatar Dangote ta buɗe sayar da hannun jarinta ga jama’a aka tara wannan kudi
  • Za a yi amfani da kuɗin da aka tara wajen ninka ƙarfin matatar ta yadda za ta iya tace ganga miliyan 1.4 a rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Masu zuba jari sun narka kudi cikin ɗan lokaci kalilan da Aliko Dangote ya buɗe sayar da hannun jarin matatar mansa.

Sayar da hannun jarin zai ci gaba tun daga yau 13 ga Satumban 2026 har zuwa ranar 13 ga Oktoba, tare da nufin tara kudi.

Kara karanta wannan

An lissafa tiriliyoyin kudin da za a kashe idan aka maido tallafin man fetur

Dangote
Aliko Dangote, da wani dauke da kudin Najeriya da matatar Dangote a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An saye hannun jarin biliyoyi a Dangote

Jaridar Business Insider ta rahoto yadda hannun jarin matatar Dangote ya yi kasuwa sosai a ranar da aka fara saida shi.

A safiyar Litinin 14 ga Satumba 2026 kamfanin ya bude saida hannun jari da nufin ya tara kudi $1.6bn (Naira tiriliyan 2.15).

Mutane da kamfanoni da-dama sun yi dafifi suna jiran wannan lokaci, kuma ana fara saida hannun jarin, suka narka kudinsu.

Da karfe 8:00 na safe aka tsara za a soma saida hannun jarin, kuma yanzu biliyoyin kudi sun shiga hannun kamfanin Dangote.

Mista Aigboje Aig-Imoukhuede ya ce daga lokacin zuwa yanzu, dubunnan ‘yan kasuwa suka sa kudinsu a cikin sa’an farko.

Aigboje Aig-Imoukhuede shi ne shugaban kamfanin Access Holdings, ya yi magana ne a wajen taron kasuwar shinko na kasa.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Dangote ya fara sayar da hannun jarin matatar shi

“Idan aka yi la’akari da wannan gagarumar dama mai cike da tarihi da kuma abin da na gani a cikin dakin tattara bayanai, inda tuni dubban masu zuba jari suka yi alkawarin zuba biliyoyin naira cikin ‘yan mintuna kaɗan ko ƙasa da awa guda, lallai abin da ku ka yi wata babbar ni’ima ce ga bil’adama.”

Matatar Dangote ta samu N10bn a 'yan mintuna

Alhaji Umaru Kwairanga wanda shi ne shugaban Nigerian Exchange Group ya yi bayanin irin kudin da aka tara zuwa yanzu.

Ya ce:

"Daga karfe 8:00 na yau, muna maganar fiye da (Naira) biliyan 10 kuma fiye da haka sun shigo."

Premium Times ta ce duk da yawan wannan kudi, bai kai 0.5% na abin da kamfanin yake so ya tara a cikin kusan kwana 30 ba.

Kuma zuwa yanzu ba za a iya cewa ko hannun jarin ya yi kasuwa ko zai yi kwantai ba, sai nan gaba za a fahimci halin da ake ciki.

Mafi girman saida hannun jari a Afrika

Rahotanni sun ce mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote, ya bude taron da karfe 9:35 a garin Legas.

Manyan attajirai da shugaban bankuna a Najeriya kamar su Jim Ovia, Benedict Okey Oramah, Adaora Umeoji sun halarci bikin.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun sake kuskuren jefa bam, an rasa rayukan jami'an tsaro

Wannan ne mafi girman hannun jari da za a saida a tarihin kasuwar shinko a nahiyar Afrika.

Dangote
Attajirin Afrika, Aliko Dangote da matatar man shi a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote za ta kafa tarihi a 2028

An rahoto cewa kamfanin Dangote zai faɗada aikin matatar daga tace ganga 700,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekaru uku.

A kokarin ganin matatar ta fi kowace girma a duniya, za a buɗe damar sayen hannun jari (IPO) ga kowa da kowa ba tare da bambanci ba.

Yanzu haka matatar tana wadatar da kasuwannin kasashen Yammacin Afirka da mai gami da fitar da man jiragen sama zuwa nahiyar Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng