Aliko Dangote Ya Fadi Abin da Zai Faru da Matatarsa nan da Shekarar 2028

Aliko Dangote Ya Fadi Abin da Zai Faru da Matatarsa nan da Shekarar 2028

  • Kamfanin Dangote yana shirin fadada matatarsa domin zama mafi girma a duniya zuwa shekara ta 2028
  • Shugagaban matatar ya suna samar da kaya a Afrika ta yamma, kuma suna fita man jiragen sama zuwa Turai
  • Kwanan nan za a bude damar sayen hannun jari (IPO) ga kowane mutum ba tare da nuna wani bambanci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Lagos - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ya ce matatarsa za ta ciri tuta a shekarar 2028.

Aliko Dangote ya ce zuwa shekarar 2028, matatarsa da ke Legas za ta zama ta fi kowace matata girma a duk fadin duniya.

Aliko Dangote
Aliko Dangote wajen wani taro a Doha Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

IPO: Aliko Dangote ya yi albishir

Attajirin ya bayyan wannan ne lokacin da yake magana wajen bikin sa hannun saida hannun jarin matatar a cewar jaridar Sun.

Dangote ya bayyana shirin saida hannun jarin matatar a matsayin wata babbar gaba ga kamafanin da ‘yan Najeriya da na Afrika.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla kan yadda za ku saye hannun jari a matatar Dangote

Ya ce a yanzu babu matata mai girmar tasa a nahiyar Afrika kuma nan gaba a shekarar 2028 za ta zama mafi girma a duniya.

Matatar Dangote za ta saida hannun jari

Game da hannun jarin da zai saida, Dangote ya ce ba a ware wasu ‘yan kasuwa ba, yake cewa kofa a bude ta ke ga duk mai sha’awa.

Da yake jawabi a ranar Litinin, mai kudin ya yi bayanin yadda bankuna suka bashi bashi ba tare da ko ganin lasisin kafa matatar ba.

An ba kamfanin Dangote aron makudan kudi lokacin da ba a ma san ina za a gina matatar ba, hakan ya nuna yadda aka yarda da shi.

"A yau an fahimci cewa babu abin da zai gagare mu muddin mu ka maida hankali kuma mu ka jajirce."

- Aliko Dangote

Burin Dangote a nahiyar Afrika

Babban ‘dan kasuwar ya ce burinsu a kamfanin Dangote Group shi ne ganin an samu masana’antu a nahiyar Afrika nan da shekarar 2030

Ya kuma ce babu yadda za a kafa masa’antu idan ba a samu isasshen makamashi a Afrika ba.

Kara karanta wannan

'Kowa zai iya saye,' Dangote ya bude kofar sayar da hannun jari a matatar shi

Jaridar The Cable ta rahoto Dangote yana bayanin yadda suka shiga Ethiopia, Kenya, Tanzania, Namibia da wasu kasashe da ke Afrika.

Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote da matatar mansa a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin Dangote a kasuwannin duniya

Shugaban matatar Dangote, David Bird, ya ce suna samar da mai ba a Najeriya kadai ba, har da sauran kasashe a Afrika ta yamma.

Bugu da kari, Mista Bird ya ce sune kan gaba wajen fita da man jirgin sama zuwa Turai.

A sakamakon rikicin da ake yi a duniya, matatar Dangote ta taimaka wajen hana mai ya yanke a gabas ta tsakiya da kasar Ukraine.

Bayani game da hannun jarin matatar Dangote

An zo da rahoto na musamman ganin an ji cewa matatar Dangote na shirin sayar da hannun jari biliyan 4.1 a kan farashin ₦525.

Sayen hannun jarin zai ba 'yan Najeriya damar mallakar kaso a kamfanin, amma ribar da za a ci ta dogara da yanayin kasuwar mai.

Masu zuba jari na buƙatar buɗe asusun dillali da na CSCS tare da duba haɗarin kasuwanci kafin sayen jari a matatar mafi girma a Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng