"Ya Yi Butulci": Gargadin da Buba Galadima Ya Yi Wa El Rufai kan Tinubu
- Buba Galadima ya zargi Tinubu da mutanensa da rashin godiya ga tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan gudunmawarsa a 2023
- Galadima ya ce ya taɓa gargadin El-Rufai ya yi taka-tsantsan, har ya ba shi shawarar barin Najeriya saboda matsalar dangantakarsa da Tinubu
- Ya kuma ce ya roƙi Rabiu Kwankwaso ya shawo kan El-Rufai kada ya dawo Najeriya, saboda ya yi zargin cewa akwai masu son cutar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Buba Galadima, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da wasu na kusa da shi da rashin nuna godiya ga tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Galadima ya ce El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Tinubu samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Naija Unfiltered Podcast, inda ya kuma yi magana kan lalacewar dangantakar da ke tsakanin Tinubu da El-Rufai.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya bukaci Atiku da Peter Obi su janyewa Tinubu, ya kawo hujja
Ya ce ya gargadi El-Rufai ya yi hattara
Buba Galadima ya ce ba shi ne babban abokin El-Rufai ba, amma ya taɓa ba shi shawarar ya yi taka-tsantsan da yadda yake tafiyar da al’amuransa.
Ya ce ya gargadi tsohon gwamnan cewa ya yi la’akari da yiwuwar barin Najeriya ko kuma fuskantar matsalolin shari’a.
Buba Galadima ya ce ya bayyana damuwarsa kan halin da El-Rufai ke ciki a wasu hirarrakin da ya yi da BBC da kuma kafafen talabijin na Najeriya.
Ya roƙi Kwankwaso ya shawo kan El-Rufai
Buba Galadima ya kuma ce lokacin da El-Rufai ya sanar da cewa zai dawo Najeriya daga Masar, ya je wurin tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, domin ya roƙe shi ya shawo kan El-Rufai kada ya dawo.
Ya ce ya gaya wa Kwankwaso cewa akwai wasu mutane da ba sa yi wa El-Rufai fatan alheri, don haka ya kamata ya yi taka-tsantsan.
A cewar Buba Galadima, Kwankwaso ya tuntubi El-Rufai, wanda daga baya ya ɗage ranar dawowarsa kafin ya sake sanar da wata sabuwar ranar dawowa Najeriya.
Buba Galadima ya ce dawowar El-Rufai jarumta ce
Galadima ya bayyana dawowar El-Rufai Najeriya a matsayin wani mataki na jarumta, musamman bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙudurin jam’iyyar APC na ci gaba da riƙe madafun iko.
Ya yi zargin cewa APC na iya amfani da kowace hanya domin ci gaba da kasancewa a kan mulki saboda abin da shugabanninta za su iya fuskanta idan suka rasa iko.
Buba Galadima ya ce wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar na sane da illar rasa mulki saboda ayyukan da ake zargin an aikata a lokacin da suke kan madafun iko.
Sai dai waɗannan kalamai zarge-zarge ne da Galadima ya yi, kuma ba su tabbatar da cewa APC ko Shugaba Tinubu na da irin wannan shiri ba.

Source: Facebook
Atiku ya yi magana kan tsare El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Bola Tinubu kan lamarin Malam Nasir El-Rufai.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnati ta yi bayani kan ci gaba da tsare Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, yana cewa lamarin ya haifar da tambayoyi kan bin ka’idojin shari’a.
Asali: Legit.ng
