Gwamna Dauda Ya Aika Sako ga Masu Rike da Mukamai a Gwamnatinsa bayan Fara Guna Guni
Gwamna Dauda Lawal ya ce jami’in da yake ganin bai amfana da gwamnatinsa ya kamata ya yi murabus daga mukaminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan more rayuwa sama da N20bn a kowace ƙaramar hukuma cikin shekaru uku
Gwamnan ya yi kira ga ’yan APC da su daina rarrabuwa zuwa gidajen siyasa tare da haɗa kai a ƙarƙashin jam’iyya guda
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙalubalanci jami’an da ke ganin ba su amfana da gwamnatinsa da su yi murabus daga mukamansu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa an gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoban 2026.
Dauda Lawal ya ce masu korafi su yi murabus
Dauda Lawal ya yi wannan magana ne bayan wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da masu rike da mukamai, matasa da mata, sun koka kan abin da suka bayyana a matsayin rashin walwala a ƙarƙashin gwamnatinsa.
Ya ce wasu masu rike da mukamai na korafin cewa ba sa samun wani abu daga gwamnati, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
“Wasu masu rike da mukamai suna korafin cewa ba su samu komai ba. Hakan ba gaskiya ba ne. Ko a cikin kwamishinoni, duk wanda yake ganin ba ya samun komai, ya yi murabus,” in ji Dauda Lawal.
An mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa
Gwamnan ya bayyana cewa cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatinsa ta fi mayar da hankali ne kan samar da muhimman ababen more rayuwa da sauran ayyuka a ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati.
A cewarsa, bayanan da gwamnati ke da su sun nuna cewa an aiwatar da ayyukan more rayuwa da suka haura N20bn a ƙananan hukumumi 14 na jihar cikin shekaru uku.
Dauda Lawal ya ce bayan shekaru uku na gudanar da mulki, samar da ayyukan more rayuwa da dawo da zaman lafiya zuwa wani matsayi, yanzu lokaci ya yi da gwamnatinsa za ta koma kan harkokin siyasa.
“Tsawon shekaru uku mun mayar da hankali kan shugabanci. Yanzu lokaci ya yi da za mu koma siyasa, domin lokacinta ya yi,” in ji shi.
Za a bayyana sunayen waɗanda aka bai wa kwangila
Gwamnan ya amince cewa kuskuren da gwamnatinsa ta yi shi ne rashin bayyana sunayen mutanen da aka bai wa kwangilolin ayyukan gwamnati.
Ya yi alkawarin cewa za a bayyana sunayen waɗanda aka bai wa kwangilolin nan ba da jimawa ba.
Dauda Lawal ya kuma ambaci wasu fitattun masu ruwa da tsaki na APC, ciki har da ’yan majalisar wakilai Abdulmalik Zannah, Ahmadu Mai-Palace, Aminu Jaji da Bello Hassan, yana cewa sun samar da kayayyakin tallafi da dama domin ƙarfafa gwiwar jama’a da matasa a jihar.
Dauda Lawal ya nemi haɗin kan ’yan APC
Gwamnan ya roƙi masu ruwa da tsaki da su yi haƙuri da ’yan siyasa da sauran magoya bayan jam’iyyar, yana mai cewa abubuwa za su sauya nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan
Magana ta fito: An ji yadda uwa da ɗiyarta suka mutu daga zuwa karbo tallafi a wurin gwamna
Ya kuma yi kira ga magoya bayan APC da su haɗa kai, tare da daina rarraba jam’iyyar zuwa gidajen siyasa daban-daban. “Daga yau, don Allah mu daina siyasar gidan wane da gidan wane. Mu haɗa kanmu a matsayin jam’iyya guda mai hangen nesa ɗaya."
“Maganar gidan Dauda, gidan Matawalle ko gidan Shehi ta daina. Mu haɗa kai mu zauna a ƙarƙashin gida guda, domin Allah ne Ya haɗa mu da ni’imarsa,” in ji Dauda Lawal.
Asali: Legit.ng

