Ana Wata ga Wata: Sabon Rikici Ya Barke a Neja, an Samu Asarar Rayuka

Ana Wata ga Wata: Sabon Rikici Ya Barke a Neja, an Samu Asarar Rayuka

  • Akalla mutane uku sun mutu bayan rikici ya barke tsakanin ’yan sa-kai da matasa a Kpakungu da Gbeganu da ke birnin Minna
  • Lamarin ya fara ne bayan wani ɗan sa-kai ya harbe wani mutum mai suna Aliyu a yayin wani samame da aka kai Kpakungu
  • ’Yan sanda sun tura jami’ai yankunan da abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargi da hannu a rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Akalla mutane uku sun mutu bayan rikici ya barke tsakanin ’yan sa-kai da wasu fusatattun matasa a Kpakungu da Gbeganu, da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Asabar, 3 ga Oktoba, lokacin da wasu ’yan sa-kai suka je Kpakungu domin cafke wasu mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Masifa ta auka wa masu hakar ma'adanai a Bauchi, an rasa rayuka

An samu barkewar rikici a Neja
Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

A cewar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, wani ɗan sa-kai ya harbe wani mutum mai suna Aliyu har lahira yayin samamen, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Mutuwar Aliyu ta janyo zanga-zanga da fusata mutane a yankin da lamarin ya auku.

Matasa sun tare hanyar Minna-Bida

Lamarin ya ƙara ta’azzara ne a farkon safiyar Lahadi, 4 ga Oktoba, lokacin da wasu matasa suka tare hanyar Minna-Bida.

Matasan sun yi hakan ne domin nuna adawa da kisan Aliyu, kafin daga bisani su nufi yankin Gbeganu.

A can ne aka ruwaito cewa wasu daga cikinsu sun kai hari kan mazauna yankin, lamarin da ya haifar da ƙarin tashin hankali.

Mutane biyu sun sake mutuwa

A yayin rikicin da ya biyo baya, an samu ƙarin mutuwar mutane biyu, wanda ya sa adadin waɗanda suka mutu ya kai uku.

Majiyoyin yankin sun ce an binne mutanen biyu da suka mutu bisa al’adun yankin. Sai dai ba a bayyana ƙarin bayanai kan mutanen da suka mutu ko kuma yadda suka rasa rayukansu ba.

Kara karanta wannan

An samu matsala, mutum 3 sun mutu a gidan gwammatin jihar Neja

’Yan sanda sun tura jami’an tsaro

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce an tura jami’ai zuwa yankunan da abin ya shafa domin tarwatsa masu tayar da rikici da dawo da zaman lafiya.

Ya ce daga bisani jami’an tsaron sun share hanyar Minna-Bida domin tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa ta ci gaba yadda ya kamata, jaridar Leadership ta dauko labarin.

Ana neman wanda ake zargin ya harbi Aliyu

Abiodun ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin cafke ɗan sa-kan da ake zargin ya harbi Aliyu har lahira.

Ya ce ana kuma neman wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen tashin hankalin da ya biyo bayan mutuwar Aliyu.

Rundunar ’yan sandan ta buƙaci mazauna yankunan da su kwantar da hankula, su kuma ci gaba da bin doka.

’Yan sandan sun tabbatar wa jama’a cewa an tura jami’an tsaro domin hana sake barkewar tashin hankali da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tattara manoma kusan 50 zuwa daji, sun nemi makudan kudin fansa

An samu rikici a jihar Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane sun mutu a gidan gwamnatin Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa akalla mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon turmutsitsi a gidan gwamnatin jihar Neja da ke Minna.

Lamarin ya faru ne lokacin da aka gayyaci wasu matasa da ake zargin suna da alaka da shirin zanga-zanga kan mutuwar masu hakar ma’adinai 37 domin su janye shirinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng