Dangote Ya Tabo Batun Hannun Jari, Ya Faɗi yadda Ƴan Najeriya Za Su Yi Arziki
- Attajiri Aliko Dangote ya ce hannayen jarin matatar Dangote da ake sayarwa kan N525 na iya kaiwa N10,000 nan gaba
- Dangote ya tabbatar da cewa kananan masu zuba jari za su samu fifiko wajen rabon hannayen jarin IPO, fiye da manyan cibiyoyin zuba jari
- An ware hannayen jari biliyan 4.1 kan N525 kowanne, yayin da mafi ƙarancin saye yake N5,250, kuma za a fara sayarwa daga 14 ga Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana kan shirin sayar da hannun jari a kamfaninsa.
Dangote ya ce hannayen jarin matatar man Dangote da ake bayarwa kan N525 kowanne na iya kaiwa N10,000 nan gaba.

Source: Getty Images
Ya bayyana hakan ne cikin harshen Hausa yayin wata hira da Abis Fulani, inda ya tattauna kan shirin IPO da fa'idodin da masu zuba jari za su samu.
Hannun jari: Ribar da mutane za su samu
Dangote ya kuma tabbatar wa kananan masu zuba jari da ke shirin shiga sayar da hannayen jarin matatar a karon farko, IPO, cewa za a ba su fifiko wajen rabon hannayen jarin.
Dangote ya ce kananan masu zuba jari da ke son sayen hannayen jari da ƙananan kuɗaɗe za su samu fifiko kan manyan masu zuba jari na cibiyoyi.
Ya ce:
“Idan aka yi irin wannan abu da ake kira IPO, kananan masu zuba jari su ne za a fara ba fifiko.
"Manyan masu zuba jari na cibiyoyi da suka nemi kaso mai yawa ba za su samu duk abin da suka nema ba. Amma kananan masu zuba jari da ke son sayen hannayen jari na N50,000, ko wasu da za su sayi na N100,000 da makamantansu, su ne za a fara bai wa fifikon rabon hannayen jari.”
Dangane da yiwuwar ƙarin darajar hannayen jarin, Dangote ya ce masu zuba jari na iya samun riba mai yawa idan darajar hannayen jarin ta ƙaru bayan an fara sayar da su a kasuwa.

Kara karanta wannan
Matasan da ake zargi da tare Peter Obi sun shiga matsala, an kwantar da mutum 10 a asibiti
Ya ce:
“Kamar yadda nake cewa, wannan hannun jari, idan ka duba, a yanzu muna kan N525. Wata rana wannan hannun jari zai kai N10,000.”
Yayin da yake bayyana yiwuwar ribar, ya ce, “Saboda haka, idan ka riƙe shi bayan ka saya, sannan ya kai N10,000, inda ka zuba N5m a baya, darajarsa za ta zama sama da N50m, ja ga, ka zama mai arziki.”

Source: Getty Images
Yadda za ka karbi ribarka cikin sauki
Dangote ya kuma ce masu hannayen jari za su iya zaɓar karɓar rabon ribarsu ko dai cikin naira ko dalar Amurka, abin da ya ce zai taimaka wajen kare su daga faɗuwar darajar kuɗin ƙasa.
Ya ce:
“Amfanin sayen wannan hannun jari shi ne, riƙe shi ba zai hana ka ci gaba da gudanar da aikinka na yau da kullum ba.
“Za ka riƙe wannan hannun jari, kuma idan aka biya riba, ba za ka buƙaci tsoron faduwar darajar kuɗi ba, za ka iya zaɓar karɓar rabon ribarka ko dai cikin Naira ko kuma cikin Dala.”
Ya ce zaɓin karɓar riba cikin dala na iya zama mai amfani musamman ga ‘yan Najeriya da ke da wasu nauyin kuɗi a ƙasashen waje.
Ya ce:
“Idan kana da yaro da ke karatu a wata makaranta a Ingila, misali, ko da akwai matsalar tattalin arziki ko faduwar darajar kuɗi — Allah Ya tsare mu — samun wannan yana nufin abin da za ka karɓa yana cikin Dala.”
Dangote ya tuna da yadda darajar naira ta ragu, inda ya ce, “Yaronka ba zai fuskanci matsalar sauyin farashin canji ba, kamar lokacin da farashin canji ya tashi daga N400 zuwa N1,800.
IPO na matatar Dangote ya ƙunshi hannayen jari na yau da kullum biliyan 4.1, inda ake sayar da kowanne kan N525.
Idan aka sayi dukkan hannayen jarin, ana sa ran za a tara kusan Naira tiriliyan 2.15, yayin da mafi ƙarancin sayen hannayen jari 10 zai ci N5,250.
Za a fara sayar da hannayen jarin ne daga ranar 14 ga Satumba zuwa 13 ga Oktoba, 2026.
Dangote ya kara farashin man fetur
Mun ba ku labarin cewa Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur da take sayarwa a farfajiyar matatar da Na85 kan kowace lita, daga N1,265 zuwa N1,350.
Karin ya zo ne yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuɗin maye gurbin man fetur ke ci gaba da tashi.
Sabon farashin ya haura matsakaicin kuɗin saukar da man fetur na yanzu da aka sanya a N1,311 kan lita, abin da ke ƙara matsin lamba a harkar mai.
Asali: Legit.ng


