Lokaci Ya Yi: Dangote Ya Fara Sayar da Hannun Jarin Matatar Shi

Lokaci Ya Yi: Dangote Ya Fara Sayar da Hannun Jarin Matatar Shi

  • Rahotanni sun bayyana cewa matatar Dangote ta sanar da fara sayar da sababbin hannun jari na 4.1bn a kan N525 kan kowane kaso, inda aka sa ran tara kusan N2.15trn
  • Kamfanin ya ce mafi ƙarancin hannun jarin da mutum zai iya saye shi ne guda 10, wanda darajarsu ta kai N5,250, yayin da sayar da hannun jarin zai kai zuwa 13 ga Oktoba 2026
  • Matatar Dangote ta ce kudin da za a samu za su taimaka wajen faɗaɗa ayyukanta, zuba jari a wasu muhimman tsare-tsare da kuma samar da ƙarin daraja ga masu hannun jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Matatar Dangote ta fara sayar da hannun jarinta ga jama’a a yau, Litinin 14 ga Satumba 2026, a wani mataki da kamfanin ya bayyana a matsayin muhimmin ci gaba ga tattalin arzikin Najeriya da kasuwannin hannun jari na Afirka.

Kara karanta wannan

Aliko Dangote ya yi bayanin abin da ya sa zai saida hannun jari a matatarsa

An shirya gudanar da bikin ƙaddamar da sayar da hannun jarin a filin cinikin hannun jari na Nigerian Exchange da ke Legas.

Alhaji Aliko Dangote
Lokacin da Aliko Dangote ke bayani a taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kamfanin ya ce wannan ne karon farko da jama’a za su samu damar mallakar wani kaso a matatar Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka.

Hannun jarin da za a sayar

Sanarwar kamfanin da aka fitar ranar Lahadi ta ce sayar da hannun jarin ya ƙunshi sababbin hannun jari guda 4.1bn, inda za a sayar da kowane kaso a kan N525.

Mafi ƙarancin adadin hannun jarin da mutum zai iya saya shi ne guda 10, wanda darajarsa ta kai N5,250.

An ce za a ci gaba da sayar da hannun jarin har zuwa ranar 13 ga Oktoba 2026, bisa sharuɗan da aka bayyana a takardar bayanan sayar da hannun jarin.

Wani sashe na matatar Dangote a Legas
Wani bangare na matatar Dangote da za ta sayar da hannun jari. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Za a tara N2.15trn

Ana sa ran sayar da hannun jarin zai samar da kusan N2.15trn, wanda zai kasance cikin manyan tallan hannun jari da aka taɓa gudanarwa a Afirka.

Kamfanin ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen bunƙasa ayyukan matatar, faɗaɗa harkokinta, gudanar da muhimman zuba jari da kuma samar da ƙarin daraja ga masu hannun jari da sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Dangote ya tabo batun hannun jari, ya faɗi yadda ƴan Najeriya za su yi arziki

An buɗe damar sayen hannun jarin ga ƙananan masu zuba jari, manyan masu zuba jari da kuma waɗanda suka cancanta a Afirka.

Batun farashin mai a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Matatar Dangote ta sake ƙara farashin fetur zuwa N1,350 kan lita, wanda ya zama mafi girman farashin da ta taɓa sanarwa tun bayan fara aiki a shekarar 2024.

Rahoto ya nuna cewa sabon farashin ya ƙaru da N85 daga N1,265 kan lita, inda matatar ta yi ƙarin farashin fetur sau huɗu tun ranar 21 ga Agusta.

Jimillar ƙarin da matatar ta yi cikin kwanaki 22 ya kai N185, wanda yake wakiltar ƙarin kashi 15.9 cikin 100, yayin da farashin ɗanyen mai na Brent ke kusan dala 104.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng