Sojojin Sama Sun Sake Kuskuren Jefa Bam, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro

Sojojin Sama Sun Sake Kuskuren Jefa Bam, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro

  • Mutane bakwai sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata bayan wani bam da ake zargin jirgin Sojin Sama ya jefa a sansanin ’yan banga a Shiroro
  • Lamarin ya faru ne yayin da ’yan bangan ke ganawa domin tsara matakin da za su ɗauka kan motsin ’yan bindiga a yankin
  • Shaidu sun ce wasu daga cikin waɗanda suka jikkata sun samu munanan raunuka, ciki har da waɗanda aka yanke wa ƙafafu biyu gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Akalla mutum bakwai daga cikin ’yan kungiyar sa-kai sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata bayan wani bam da ake zargin wani jirgin Sojin Saman Najeriya ya jefa a jihar Neja.

Ana zargin cewa dai jirgin saman sojojin ya jefa bam din ne a yankin Kukoki-Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

Sojojin sama sun kai hari a Neja
Jirgin saman rundunar sojojin sama ta Najeriya Hoto: @NigAirforce
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 10 ga watan Satumban 2026 a wani sansanin ’yan bangan, waɗanda aka fi sani da DSS Hunters.

An jefa bam din ne yayin da 'yan bangan suke ganawa domin tsara matakin da za su ɗauka kan rahotannin motsin ’yan bindiga a kusa da yankin.

An garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti

Majiyoyi sun ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna domin ba su kulawar gaggawa.

An ce wasu daga cikin waɗanda suka samu raunukan sun ji munanan rauni, inda wasu suka rasa ƙafafunsu biyu gaba ɗaya sakamakon fashewar bam ɗin.

Kwamandan ’yan bangan yankin Kukoki, Ayuba Umar Kamas, ya ce sun ga jirage uku a sararin samaniyar yankin kafin lamarin ya faru.

Jirgin sama ya jefa bam kan sansanin

Ayuba Umar Kamas ya ce ɗaya daga cikin jiragen ya yi shawagi a kan inda suke sannan ya jefa bam ɗin, wanda ya faɗa kan sansaninsu.

Kara karanta wannan

An dauki mummunan mataki kan malamin addini bisa zargin batanci ga iyayen manzon Allah

Ya bayyana cewa mutum bakwai da suka mutu sun haɗa da huɗu daga Kukoki, ɗaya daga Bassa da kuma wasu uku daga Matuku.

Kwamandan ya nuna takaicinsa kan yadda harin ya shafi sansaninsu a daidai lokacin da ake zargin ’yan bindiga na wucewa a yankin cikin walwala.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kasance kusan 250 a kan babura, yayin da suke tafiya da shanun da ake zargin sun sace, Daily Post ta kawo rahoton.

Ana zargin an yi kuskure wajen kai hari

Majiyoyin yankin sun ce mai yiwuwa jami’an sojojin sama sun samu bayanan sirri kan motsin ’yan ta’adda a yankin, amma suka yi kuskure wajen gano inda ya kamata su kai harin.

An kuma ce bayan faruwar lamarin, an fara kwashe waɗanda suka jikkata da babura kafin daga bisani a kai su asibitin IBB Specialist Hospital da ke Minna domin samun magani.

Sojojin sama sun kai hari a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojojin sama sun samu kayan aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka ta kawo kayan aiki da suka kunshi makamai da sauransu ga Rundunar Sojin Sama​ ta Najeriya.

Amurka ta shigo da kayan aikin Najeriya ne domin tallafa wa rundunar sojojin sama wajen yaki da kungiyoyin yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng