Sheikh Gumi: Matar Morocco Ta Fito Ta Fadi Abin da Ya Faru da Kanta a Bidiyo
- 'Yar kasar Morocco, Khadija Diab, ta yi bayani kan rikicin aurenta da Nasiru Idris Musa, inda ta musanta wasu daga cikin bayanan da mijin nata ya gabatar a kafafen sada zumunta
- Khadija ta ce ita ce ta fara barin gidan mijinta, tana mai cewa ta yanke shawarar ba za ta sake zama tare da shi ba saboda matsalolin da ta ce ta fuskanta a cikin aurensu
- Ta kuma bayyana cewa Sheikh Ahmad Gumi ya taba shiga tsakani domin sulhunta tsakaninta da mijinta fiye da sau daya, yayin da malamin din ya yi kira kan shari'ar da suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – Matar Nasiru Idris Musa, ‘yar kasar Morocco, Khadija Diab, ta fito ta yi karin haske kan rikicin aurenta da mijinta, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan wasu bayanai da aka yada a kafafen sada zumunta.
Khadija ta ce ita ce ta fara barin gidan mijinta, tana mai cewa ta fi son ta mutu idan ba ta samu tallafi da taimako bayan ta bar gidan ba.

Source: Facebook
A bidiyon da Dr Gumi ya wallafa a Facebook, ta zargi mijin nata da yawan yin karya, cin mutuncinta da zaginta.
Korafin da matar ta yi
Ta yi zargin cewa bayan aurensu da zuwansu Najeriya ne ta fara fahimtar cewa wasu daga cikin abubuwan da ya fada mata kafin aure ba gaskiya ba ne.
Ta ce Nasiru ya taba yi mata alkawarin zai samar mata da gida na kanta, amma hakan bai tabbata ba. Haka kuma ta ce ya bukace ta da ta zauna tare da matarsa ta farko, abin da ta ki amincewa da shi.
Khadija ta kuma ce ba ta saba da wankin kaya ba, inda ta bayyana cewa hakan ya zama daya daga cikin matsalolin da suka samu a zamantakewarsu.
Ta ce lokacin da ta kamu da rashin lafiya, ba ta samu kulawar da ta kamata daga mijinta ba, domin a cewarta, da kyar yake kai ta asibiti domin neman magani.
Khadija ta kara bayyana cewa Nasiru ya kwace mata fasfon da take amfani da shi wajen tafiya zuwa kasarta ta Morocco, tana mai cewa hakan ya kara mata wahalar komawa gida.
Ta ce mijin nata ya nuna mata wani salon rayuwa da kuma aikin da ya ce yana yi kafin aurensu, amma daga baya ta gano cewa abubuwan da ya gabatar mata ba su kasance kamar yadda ya bayyana ba.
Sheikh Gumi ya taba shiga tsakani
Khadija ta bayyana cewa Nasiru Musa yana da matukar girmama Sheikh Ahmad Gumi, kuma a lokutan bukukuwan Sallah da makamantansu, ya kan kai ta wajen malamin domin ziyara.
Ta ce a wasu lokutan da sabani ya shiga tsakaninta da mijinta, Nasiru ya kai ta gidan Sheikh Gumi, sai dai ta ce Sheikh Gumi ya shiga tsakani domin sasanta su fiye da sau daya a lokacin da suke fuskantar matsalolin aure.
Kiran da Sheikh Gumi ya yi
Bayan bayanin matar, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa “matar Morocco ta yi magana”, inda ya mayar da hankali kan bukatar gaggauta magance matsalar aurenta ta hanyar tsarin Shari’a.
Sheikh Gumi ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya yi amfani da matsayinsa wajen gaggauta neman shiga tsakani daga kotun Shari’a, domin a dauki matakin da ya dace kan wannan aure da ake zargin yana haddasa wahala.
Ya ce matar ta riga ta sha wahala, don haka bai kamata a bar ta ta ci gaba da fuskantar wahala ba saboda jinkirin tsarin da aka kafa domin tabbatar da adalci da kariya.
Ya kuma bayyana cewa matar na bin Nasiru Musa Idris wasu kudi nata na kashin kanta da ya karba amma bai biya ba.
A cewar Sheikh Gumi, a irin wannan yanayi, ba zai dace a tilasta wa matar ta sake biyan mijinta wani kudi a matsayin sharadin samun rabuwar aure ta hanyar khul’u ba.

Source: Original
Bayanin da lauya ta yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata ‘yar kasar Morocco, Khadija Diab ba ta tare da malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi, kamar yadda lauyarta, Bilkisu Abdulrasheed Chedi, ta bayyana.
Lauyar ta ce Khadija ta kasance a kasar Morocco tun watan Afrilu na 2026, bayan kungiyar Women Aware of Rights Initiative ta taimaka mata wajen samun takardar tafiye-tafiye ta gaggawa.
Chedi, wadda ita ce shugabar kungiyar, ta ce an samar mata da takardar ne bayan zargin cewa mijinta ya kwace mata fasfon kasa da kasa, lamarin da ya hana ta komawa kasarta cikin sauki.
Asali: Legit.ng


