Sanata Shehu Buba Ya Fito Fili Ya Yi Magana kan Zargin Hannu a Ta'addanci
- Sanata Shehu Buba ya yi martani kan zargin cewa yana daukar nauyin ’yan bindiga kamar yadda wasu ke yada bidiyoyi
- Shehu Buba ya ce ya dade yana fuskantar farfaganda, labaran karya da bidiyoyin bogi, musamman tun 2024, kuma ya shigar da kara kan masu yada su
- Sanatan ya ce tun bayan zama dan takarar gwamna karkashin PRP a Bauchi, yakin bata sunansa ya kara tsananta, amma zai kare kansa ta hanyar doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sanata Shehu Buba, ya yi ƙarin haske kan zarge-zzargen da ake yi masa cewa yana ɗaukar nauyin yan bindiga a Najeriya.
Sanata Shehu Buba ya ce ba shi da hannu cikin ’yan bindiga, kuma ba ya daukar nauyinsu ta kowace hanya.

Source: Facebook
Buba ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da bayanai dalla-dalla da ya fitar a Abuja, bayan sake bullar wasu bidiyoyin da aka shirya domin bata masa suna, cewar TheCable.
Buba ya ce tun daga shekarar 2024 yake fuskantar farfaganda, labaran karya da bidiyoyin bogi a Bauchi da sauran wurare.
Domin kare mutuncinsa, ya ce ya shigar da kararraki kan wadanda ke yada labaran karya a kotunan Najeriya da kuma birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.
Ya ce “manyan jagororin ’yan bindiga” ba su taba ziyartar gidansa ba, sannan bai dauki nauyin wani daga cikinsu zuwa aikin Hajji ba.
Sanatan ya ce yakin bata sunansa ya kara tsananta tun bayan da ya zama dan takarar gwamna na Peoples Redemption Party (PRP) a Bauchi.
Ya ce:
“Shawarata ta barin APC zuwa PRP karkashin inuwar da nake neman kujerar gwamna, ya kamata a yi muhawara a kai bisa manufofi, kwarewa da hangen nesa—ba bisa zarge-zargen kirkira ba.”
Sanatan ya yi Allah wadai da kokarin bata masa suna da kuma rage kimar aikin kishin kasa da yake yi wa Najeriya.
Ya ce:
“Abin takaici ne matuka idan aka cire ayyukan tausayi ko halastattun hulda da suka shafi tsaro daga mahallinsu, sannan a sake tsara su domin a gabatar da su a matsayin hujjar aikata laifi.

Kara karanta wannan
Bayanai sun fito da aka zargi Ahmad Gumi da dauke matar da wani ya auro daga Morocco
“Ina maraba da bincike, amma dole ne binciken ya kasance na adalci. Ba na ikirarin cewa ba za a bincike ni ba..
A matsayina na Sanata, tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Kasa da Leken Asiri, kuma yanzu Shugaban Kwamitin kan Kiwo da Kula da Dabbobi, sannan dan takarar gwamna, na fahimci cewa za a binciki ayyukana da alaka ta. Wannan shi ne dimokuradiyya.
Dalilin da ya sa bai yi magana a baya ba
Buba ya bayyana dalilin da ya sa ya dade bai yi magana a bainar jama’a kan wadannan zarge-zarge ba.
Ya ce a irin wannan yanayi ne ya fara kin mayar da martani ga bidiyoyin da ake yadawa, wadanda ake cewa suna nuna “manyan jagororin ’yan bindiga” suna ziyartar gidansa.
Sai dai ya ce saboda ci gaba da sake yada bidiyoyin, tare da kara tsananta zarge-zargen, ya zama wajibi ya bayyana gaskiyar lamarin ga ’yan Najeriya.
Sanata Buba ya shiga kotu da matashi
Mun ba ku labarin cewa Sanata Shehu Buba Umar ya bukaci hukumomi su gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake masa na alaƙa da ’yan ta’adda.
Sanatan ya kalubalanci Hassan da ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike na doka.
Masu goyon bayan Shehu Buba sun ce ba za su amince da amfani da kafafen sada zumunta wajen yada zarge-zargen da ba a tabbatar ba.
Asali: Legit.ng

