Fitacciyar Jarumar Fim, Zainab Diamond Ta Rasu bayan Sallar Asuba

Fitacciyar Jarumar Fim, Zainab Diamond Ta Rasu bayan Sallar Asuba

  • Rahotanni sun bayyana cewa jarumar shirin Labarina, Zainab Diamond, wadda aka fi sani da Maman Bintalo, ta rasu bayan fama da doguwar jinya
  • Wasu bayanai da Legit ta samu sun nuna cewa jarumar ta rasu ne bayan Sallar Asuba ta yau, lamarin da ya jefa abokanta da masoyanta cikin alhini
  • Abokai da masoyan jarumar sun yi ta addu’o’i da neman Allah Ya gafarta mata, Ya jikanta da rahama, Ya kuma sanya Aljanna ce makomarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Jarumar shirin fim din Hausa na Labarina, Zainab Diamond, wadda aka fi sani da Maman Bintalo, ta rasu bayan fama da doguwar jinya.

An ruwaito cewa rasuwar jarumar ta faru ne bayan Sallar Asuba ta yau, inda labarin ya jefa ‘yan uwa, abokan aiki da masoyanta cikin jimami.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Fitacciyar jarumar Kannywood da ta fito a shirin Daɗin Kowa ta rasu

Jaruma Zainab Diamond
Jarumar fim da ta rasu, Zainab Diamond. Hoto: Zahra Aliyu
Source: Facebook

An sanar da rasuwar Zainab

Kawarta, Zahra Aliyu, ta wallafa sanarwar rasuwar a Facebook, inda ta bayyana Zainab Zee Diamond a matsayin abokiyarta.

Ta rubuta cewa:

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji'oon! Cikin alhini na ke sanarda ku cewa, Allah Ya Amshi rayuwar abokiyata Zainab Zee Diamond.
“Ta rasu bayan sallar Asuba din yau bayan tayi fama da doguwar jinya.
“Allah ya miki rahama Zainab.”

Aminiya ta wallafa cewa wasu daga cikin jarumar Kannywood sun yi ta'aziyyar rasuwar jarumar., inda suka roki Allah ya gafarta mata.

Daya daga cikin abokan aiki da ya nuna matukar damuwa kan rasuwar shi ne Real Buroshi Mawaka Sokoto, inda shi ma ya tabbatar da cewa ta yi jinya.

An tabbatar da ta rasu

Abdul M Shariff ya tabbatar da rasuwar jarumar a wata tattaunawa da Legit Hausa, inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Abba Kabir Yusuf zai karfafi 'yan Kannywoo

Ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayiyar da kuma abokan aikinta, yana mai roƙon Allah Ya gafarta mata, Ya kuma ba iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi.

“Lallai an yi babban rashi. Allah ya jikanta, ya gafarta mata. Allah ya ba iyalanta hakuri,”

In ji Abdul Ma Shariff.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Masoya sun cika kafafen sada zumunta da addu’o’i bayan samun labarin rasuwar da safiyar ranar Litinin, 7 ga Satumban 2026.

Bayan sanarwar rasuwar, masoya da masu bibiyar ayyukan jarumar sun yi ta bayyana alhininsu tare da yi mata addu’a.

Wasu daga cikin addu’o’in sun haɗa da roƙon Allah Ya jiƙanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljanna ce makomarta, sannan Ya bai wa iyalanta haƙuri.

Abba zai tallafi 'yan Kannywood

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafa wa Kannywood da sauran masu fasaha.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa mawaka, masu shirya fina-finai, ‘yan fim da sauran masu fasaha domin bunkasa hazakarsu da dogaro da kai.

Ya bayyana masana’antar a matsayin muhimmiyar hanya wajen ƙarfafa matasa, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa al’adun Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng