Bayanai Sun Fito da Aka Zargi Ahmad Gumi da Dauke Matar da Wani Ya Auro daga Morocco
- Nasiru Musa Idris ya zargi Ahmad Abubakar Gumi da hana jami'an tsaro binciken batan matarsa 'yar Morocco
- Babban malamin ya karyata zargin, inda ya bayyana aniyarsa ta shigar da ƙarar Nasiru gaban kotu saboda bata masa suna
- Hadimin Sheikh Gumi ya tabbatar da matar ce da kanta ta zo neman dauki, kuma a yanzu tana tare da iyayenta a Morocco
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Nasiru Musa Idris wani ‘dan kasuwa da ya auri mata daga kasar waje, ya zargi Ahmad Abubakar Gumi da raba shi da ita.
Alhaji Nasiru Musa Idris ya zargi Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da karbe masa mata, kuma ya hana jami’an tsaro su binciki batun har yau.

Source: Facebook
'Dan kasuwa ya jefi malami da zargi mai nauyi
A wata hira da aka yi da Nasiru Idris a gidan rediyon RFI, ya bada labarin yadda ya hadu da Ahmad Gumi da yadda ya shiga harkar aurensa.

Kara karanta wannan
Bayan ƙalubalantar shi kan gina jami'a a Arewa, Atiku ya ce ba domin riba ya yi ba
‘Dan kasuwan ya ce ya auro matarsa ne daga kasar Moroko, kuma lokacin da suka hadu ba ta san Sheikh Gumi ko wani a Najeriya ba.
Ya yi ikirarin ya auri wannan balarabiya ne kamar yadda doka ta tanada, amma daga baya aka tado maganar takardar shaidar aure.
Mutumin ya ce lamarin ya kai Gumi ya bukaci a raba aurensu kuma ya yi kokarin hana jami’an tsaro su bincike bacewar matar tasa.
Ahmad Gumi ya karyata zargin boye matar aure
Da Daily Trust ta zanta da babban malamin Musuluncin, ya karyata wadannan zargi da aka yi masa na raba Nasir da mai dakinsa.
Har ta kai Sheikh Gumi ya kuma bayyana cewa zai yi karar wannan mutumi a gaban kotu.
Sai dai da aka nemi jin cikakken abin da ya faru daga bakinsa, malamin bai yi wata magana ba, illa ya ce dama ana shari’a kan zancen.
Da gaske matar tana gidan Sheikh Gumi?
A karin bayanin da ya yi aka fahimci cewa matar mutumin ba ta hannun shi, tuni ta koma kasar da ta fito, tana can tare da iyayenta.
“Amma zan kai shi kotu saboda bata mani suna. A game da yarinyar kuwa, ta bar Najeriya tuni kuma yanzu haka tana Moroko hankalinta kwance tare da iyayenta.”
“Ban so inyi magana sosai game da zancen da yake kotu, amma zan yi karar shi saboda bata suna.”
- Ahmad Gumi

Source: Facebook
Shaida daga bakin wani na kusa da malamin
Wani hadimi na malamin kuma shugaban ‘yan agaji a Masallacin Sultan Bello, Malam Nasiru Ayuba, ya karyata zargin da ake ji.
Malam Nasiru Ayuba ya ce Gumi bai boye matar a gidansa ba, illa ita ce ta kawo kukanta wajen shi a lokacin tana neman taimako.
Ganin cewa yar kasar waje ce, dan agajin ya ce sai Dr. Gumi ya taimake ta, har ta shigar da kara a kotu
Sheikh Gumi ya karyata zargin da ake yi
Sheikh Ahmad Gumi ya kare kansa daga zargin cewa yana da hannu ko yana kokarin tsoma baki a batun sace 'yan makaranta a Oyo.
Ya bayyana cewa ziyarar da ya kai Ibadan ta kasance ne domin wakiltar gamayyar malaman Musulunci na Arewa, ba kan sha'anin tsaro ba.
Malamin ya kuma jaddada goyon bayansa ga kungiyar MURIC wadda ta musanta rahotannin cewa masu garkuwa sun nemi kafa shari'a.
Asali: Legit.ng

