Ranar Yanci: Atiku Ya Dauko Batun da Yan Najeriya ke Bukatar Sani kan Raba Tallafin N75,000
- Atiku Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi wa yan najeriya bayanain yadda shirin tallafin N75,000 y isa ga talakawa
- Hakan na zuwa ne bayan shugaaban APC, Nentawe Yilwatda ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan 10 sun samu N75,000 kowannensu
- Atiku ya bukaci a bayyana yadda aka tantance wadanda suka amfana da kudin da kuma yadda aka biya su wadannan kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan shirin tallafin kudi na CCT, wanda ake raba wa mutane N75,000.
Atiku ya nemi gwamnatin Tinubu ta fito ta yi gamsasshen bayani kan yadda aka bai wa kowane dan Najeriya da samu damar dhiga shirin tallafin N75,000.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan Shugaban Jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan 10 sun samu N75,000 kowannensu.
Abin da shugaban APC ya fada
Yilwatda ya bayyana hakan a ranar 26 ga Satumba, 2026, yayin da yake magana da manema labarai bayan taron kwamitin zartarwa na kasa na APC a Maiduguri, Jihar Borno.
Ya ce wadanda suka amfana talakawa ne da masu rauni, wadanda mafi yawansu ba su da wayoyin hannu, talabijin ko damar amfani da kafafen sada zumunta.
“Mun bai wa sama da ’yan Najeriya miliyan 10 N75,000 a fadin kasar nan ta hanyar shirin tallafin kudi na CCT karkashin Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci.”
"Idan kuka lissafa, kowane mutum guda daga cikin mutane miliyan 10 ya karbi N75,000, adadin kudin da aka raba wa talakawa ya kai akalla Naira biliyan 750."
Atiku ya bukaci bayani daga gwamnati
Atiku ya bukaci gwamnatin ta yi bayani kan yadda aka tantance wadanda suka cancanta, aka aiwatar da biyan kudin sannan aka kai musu kudin, musamman a yankunan da matsalar tsaro ta shafa.

Kara karanta wannan
Nigeria @66: Cikakken jawabin da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a ranar samun 'yancin kai
Atiku ya ce:
“Akwai ikirarin shugaban jam’iyyarku cewa sama da ’yan Najeriya miliyan 10 sun samu N75,000 kowannensu ta hanyar tallafin kudi — wanda ya kai akalla N750 biliyan gaba daya.”
“Farfesa Yilwatda ya ce da yawa daga cikin wadanda suka amfana ba su da wayoyi. To, ta yaya gwamnatin ku ta tantance su, ta tuntube su kuma ta ba su kudin, musamman a wasu sassan Yobe da Borno inda matsalar tsaro ta hana zuwa wuraren?”
Atiku ya tambayi ko an ba wadanda suka amfana kudin ne da hannu ko kuma ta hannun cibiyoyin hada-hadar kudi, yana mai bukatar a gabatar da takardun da ke tabbatar da kowace hanya da aka bi.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa bukatarsa ita ce a samar da cikakken tsarin bayanan biyan kudin da za a iya bincikawa, ba wai a fadu bayanan sirrin wadanda suka amfana ba.
Ya kara da cewa:
“Idan kun iya zakulo mutane miliyan 10 da za ku bai wa tallafin, to ya kamata ku iya yin bayanin yadda aka raba masu kudin.”
Atiku ya soki shirin karbo sabon bashi
Kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi bayani kan yadda aka kashe kudin da Najeriya ta ci bashi kafin neman sabon bashin dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya.
Atiku ya ce bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 166.79, yana mai tambayar gwamnatin tarayya dalilin ci gaba da neman karin bashi dukNda ikirarin samun karin kudin shiga
Asali: Legit.ng

