An Gano Yadda ake Cinikin Yara bayan Kama Uwa Mai Sayar da 'Ya'yanta

An Gano Yadda ake Cinikin Yara bayan Kama Uwa Mai Sayar da 'Ya'yanta

  • Wata da ake zargi da hannu a safarar yara a Jihar Oyo, Adejoke Popoola, ta bayyana yadda ta sayar da wasu daga cikin yaran da ta haifa tare da sace wasu
  • Popoola ta ce ta fara shiga harkar tun watan Oktoban 2024, inda ta amsa cewa ta sayar da jariri da kuma wasu tagwaye da ta haifa da kanta
  • A bayana da ta yi wa 'yan sanda, ta kuma amsa cewa ta sace yara 19, inda ta ce shida daga cikinsu sun mutu yayin da sauran 13 suke raye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo – Wata da ake zargi da kasancewa a ƙungiyar satar yara da safarar su, Adejoke Popoola, ta bayyana yadda ta sayar da yaran da ta haifa da kuma yadda ta sace wasu yara domin sayar da su.

Kara karanta wannan

An yi ta jifan Peter Obi da magoya bayansa yayin ziyarar ta'aziyya a Benue

Popoola ta bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da take magana da manema labarai a hedikwatar rundunar ’yan sandan Jihar Oyo da ke Ibadan.

Yaron da aka ceto a Oyo
Yaran da 'yan sanda suka ceto a jihar Oyo. Hoto: Oyo State Police Command
Source: Facebook

A sakon da ta wallafa a X, rundunar 'yan sanda ce ta shafe tsawon lokaci tana gudanar da wannan aiki, inda ta fara tun watan Oktoban 2024.

Ta sayar da jariri da tagwaye

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Popoola ta ce ta haifi yara bakwai, ciki har da wasu da suka riga suka yi aure. Ta ce ɗanta na ƙarshe yana da shekaru shida, yayin da babbanta ke da shekaru 34.

Ta bayyana cewa ta sayar da jariri namiji da kuma tagwaye a shekarar da ta gabata, inda ta ce wani asibiti a Ogeere ya sayi tagwayen kan N300,000.

Ta ce:

“Allah ya ba ni baiwar samun ciki. Duk lokacin da wani namiji ya yi jima’i da ni sau biyu, nakan samu ciki, kuma yana da wahala in zubar da shi.
“Na sayar da yara biyu, jariri namiji da kuma tagwaye a bara. Na sayar da tagwayen ga wani asibiti a Ogeere, wanda shi ma yake sake sayar da su ga kwastomominsa a Legas.

Kara karanta wannan

Dan Kano ya yi wakar zaman lafiya da harsuna 11 ya isar da sako ga duniya

“Asibitin da ke Ogeere ya ba ni N300,000 kan tagwayen.”

Yadda take satar yara

Popoola ta kuma amsa cewa tana satar yara, inda ta bayyana yadda take amfani da wata dabara wajen shiga gidajen mutane.

Ta ce wani lokaci tana zuwa gidan mutane ta bayyana cewa tana neman hayar gida, sannan idan ba ta ga manya ba, sai ta ɗauki yaran da ta gani.

Ta ce:

“Ina satar jarirai. Zan je gidansu in ce ina son yin hayar gida. Idan ban ga kowa ba, kuma na ga ’ya’yansu, sai kawai in sace yaran.”

’Yan sanda sun ceto yara

Punch ta ruwaito cewa rundunar ’yan sandan jihar Oyo ta gano wata ƙungiyar satar yara da safarar su da ke aiki a jihohi daban-daban.

A bayanin da ta yi a Oyo, rundunar ta ce ta ceto yara 17 tare da kama mutane bakwai yayin binciken lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Oyo, Abimbola Olugbenga, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Eleyele, Ibadan.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Buba ya fito fili ya yi magana kan zargin hannu a ta'addanci

Olugbenga ya ce binciken ya fara ne bayan samun wata takarda ta ƙorafi, amma daga baya ya gano wata babbar hanyar aikata laifi da ake zargin ta ƙunshi satar yara, safarar su, sayar da su da kuma ɓoye su.

Mutanen da aka kama suna satar yara
Mutanen da 'yan sanda suka kama da zargin satar yara a Oyo. Hoto: Oyo Police Command
Source: Facebook

Olugbenga ya ce Popoola ta ambaci Adekanbi Janet, wadda aka fi sani da Hosanna, a matsayin abokiyar hulɗarta.

An ceto yara a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya ta ceto jarirai biyu da aka yi watsi da su a wurare daban-daban a Kurudu da Gwagwalada.

An gano jaririn namiji a Kurudu bayan wani mazaunin yankin mai suna Innocent ya ji kukan jariri kusa da Obodo, inda aka same shi an nannade shi da zane a cikin kwalin kwali.

A Gwagwalada kuwa, wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim ya ji kukan jariri a wajen gidansa da daddare, inda aka gano jaririyar mace aka kai ta asibiti domin samun kulawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng