Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutane, Sun Maida Garuruwa 15 Kango a Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutane, Sun Maida Garuruwa 15 Kango a Jihar Katsina

  • Aƙalla garuruwa 15 a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina sun zama kango sakamakon sababbin hare-haren 'yan bindiga
  • Mazauna Funtua, Dandume da Bakori sun ce matsalar tsaro ta ƙara ta'azzara tare da hana mutane gudanar da ayyukansu
  • Wasu mazauna yankin sun yi ikirarin cewa sama da mutum 100 aka yi garkuwa da su cikin makonni biyu a Dandume

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Aƙalla garuruwa 15 a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina sun zama kango watau babu kowa a ciki sakamakon karuwar hare-haren da 'yan bindiga a yankin.

Mazauna yankunan sun shaida cewa hare-haren sun kuma ƙaru a ƙananan hukumomin Funtua, Dandume da Bakori, musamman a al'ummomin da ke kudancin jihar.

Katsina.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen yankin sun ce tabarbarewar tsaro ta sanya su cikin fargaba, tare da hana su zirga-zirga da kuma kawo cikas ga noma da sauran harkokin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri a Arewa, hatsabibin dan bindiga ya bakunci lahira a Zamfara

Wani mazaunin Funtua ya bayyana cewa 'yan bindiga suna kai hari a wasu sassan garin duk da kasancewar jami'an tsaro.

Hare-hare sun ƙaru a Funtua

Ya ce:

"Yadda abubuwa suke faruwa yanzu ya nuna babu inda 'yan bindiga ba za su iya kai hari ba a garin Funtua. Kwanan nan sun je Unity Bank, suka kwace shanu suka tafi da su."

Mazaunin ya ce jami'an tsaro sun kuma yi musayar wuta da 'yan bindigar ranar Alhamis lokacin da suka yi yunkurin kwace shanu a yankin MTD.

"Sun kuma shiga unguwar Shanu, inda suka yi musayar wuta da jami'an tsaro kafin daga bisani aka fatattake su. An kashe ɗaya daga cikin 'yan bindigar, yayin da su ma suka kashe mutum ɗaya.
"Sai dai jami'an tsaro suna ƙoƙari. Duk lokacin da aka kira su, suna amsawa tare da ba da taimako," in ji shi.

Mazauna Bakori sun koka

A Bakori kuma, mazauna garuruwa da ƙauyuka fiye da 10 da suka hada da Kakumi, Sabon Layi, Gidan Jaura da Garanguzai sun nuna damuwa kan ci gaba da hare-haren.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun fatmaki mutane ana shirin yin sallah, an rasa rayukan bayin Allah

Wani mazaunin yankin ya ce 'yan bindiga sun sanya zirga-zirga tsakanin al'ummomin yankin cikin hatsari.

Ya ce:

"Har yanzu muna fama da wadannan mutane. Idan ka yi tafiyar kusan kilomita ɗaya daga cikin gari, za ka iya cin karo da su. Ko dai su harbi mutum ko kuma su kwace babur ɗin da yake hawa.

'Yan bindiga sun addabi Dandume

A Dandume, wani mazaunin yankin ya ce lamarin ya ƙara tsananta, inda ake zargin 'yan bindiga da kai hare-hare kusan kullum.

Ya ce:

"A cikin makonni biyu da suka gabata, babu ranar da 'yan bindigar nan ba su shigo ƙaramar hukumar ba domin su kashe mutane, su yi garkuwa da su ko kuma su kore su daga gonakinsu ko gidajensu.

Ya yi ikirarin cewa an yi garkuwa da sama da mutum 100 a yankin cikin makonni biyu, yayin da da dama daga cikinsu ke ci gaba da zama a hannun 'yan bindigar.

Ya ce:

"Lokacin da suka yi garkuwa da ɗana ma, sai da na biya kuɗin fansa kafin aka sake shi. A wannan lokacin ne kuma suka tafi da shanu sama da 30."

Kara karanta wannan

An kama dalolin bogi na Naira miliyan 30 ana kokarin shiga da su jama'a

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a wurin kaddamar da jami'ar rundunar C-Watch Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Garuruwa 15 sun zama kango

Aminiya ta ruwaito cewa hare-haren da ake ci gaba da kaiwa sun tilasta wa mazauna wasu al'ummomi tserewa zuwa wuraren da suka fi tsaro, lamarin da ya sa wasu ƙauyuka suka zama kango.

Wani mazaunin Dandume ya ce kusan garuruwa 15 sun zama babu kowa a cikinsu.

Ya ce:

"Na san kusan garuruwa 15 da a halin yanzu babu mutum ko ɗaya da yake zaune a cikinsu. Babu gidajen da ake zaune, babu mutane, babu komai. Sun zama kango.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

Sojoji sun kashe yan bindiga a Katsina

Kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar ’yan ta’adda ta Kachalla Muhammadu Filan a Katsina.

An kashe kwamandojin biyu, Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, da Umar Bocho, yayin wani samame da sojoji suka gudanar a kusa da ƙauyen Kogo da ke Ƙaramar Hukumar Matazu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262