'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Katsina, Dubunnan Mutane Sun Tsere daga Gidajensu

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Katsina, Dubunnan Mutane Sun Tsere daga Gidajensu

  • Sama da mazauna Unguwar Guru 3,000 sun tsere daga gidajensu bayan sabbin hare-haren ‘yan bindiga a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina
  • Mazauna sun ce an kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata a hare-haren da aka kai ranar Asabar da Litinin
  • ‘Yan gudun hijirar sun kwashe sama da kwanaki tara a Rimaye ba tare da samun wani tallafi daga gwamnatin jihar ko tarayya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Sama da mazauna Unguwar Guru da ke gundumar Sukuntuni a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina 3,000 sun tsere daga gidajensu bayan sabbin hare-haren ‘yan bindiga.

Hare-haren baya-bayan nan sun faru ne ranar Asabar da Litinin, inda aka kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata da dama.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya gayawa mutane abin da za su yi a kawo karshen 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kak hare-hare a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Mazauna da suka rasa matsugunansu, wadanda suka kwashe sama da kwanaki tara a garin Rimaye, sun shaida wa Daily Trust cewa sun bar gidajensu ba tare da daukar kusan komai ba, kuma har yanzu ba su samu wani tallafi daga gwamnatin jihar Katsina ko gwamnatin tarayya ba.

Mutanen na bukata tallafi

Muhammadu Lurwanu, wani mazaunin Unguwar Guru, ya ce an tilasta wa daukacin al’ummar da ta kunshi sama da mutane 3,000 barin gidajensu bayan hare-haren.

Ya roki gwamnatin jihar Katsina da ta gaggauta daukar mataki tare da samar da abinci, tufafi, ruwa da sauran kayan agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu.

“Dukkan mutane sun gudu daga Unguwar Guru. Mun fi mutum 3,000, kuma yanzu mun watse a wurare daban-daban. Wasu suna zama a gine-ginen da ba a kammala ba, yayin da wadanda ke Rimaye suke samun mafaka a makarantar firamare ko kuma suna tare da ‘yan uwansu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Yadda walkiya ta fado kan mata mai ciki ta mutu har lahira a Bauchi

Wani mazaunin yankin, Yahaya Matsiga, ya bayyana halin da suke ciki a matsayin “mai matukar tsanani da ban tausayi”, yana mai cewa iyalan da suka rasa matsugunansu na bukatar agajin jin kai cikin gaggawa.

Ya zuwa karfe 3:00 na rana ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026, mutanen sun ce wasu daga cikinsu ba su ci ko abinci guda ba.

Sun ce an kona gidajensu a yayin hare-haren, yayin da iyalai da dama suka rabu kuma ba su san inda wasu daga cikin ‘yan uwansu suke ba.

Gwamnati na jiran rahoto

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Katsina ta ce tana jiran cikakken rahoto daga hukumomin yankin kan harin da aka kai Unguwar Guru.

Babban mataimaki na musamman ga Gwamna Dikko Umar Radda kan harkar ‘yan bindiga, Sa’idu Ibrahim Danja, ya ce gwamnatin jihar ba ta samu rahoto daga hukumomin yankin da abin ya shafa ba.

Mutane sun bar gidajensu a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Danja ya ce gwamnati za ta fi samun damar tantance matakin da ya dace ta dauka bayan ta samu rahoton daga hukumomin yankin.

Shugaban karamar hukumar Kankia, Alhaji Salisu Gizy, bai amsa kiran waya da sakonnin kar ta kwana da aka aika masa ba domin jin ta bakinsa kan harin da kuma gudun hijirar mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi wa 'yan bindiga rubdugu a Katsina yayin dakile mummunan shirinsu

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami’an tsaro sun hallaka akalla ‘yan bindiga 24 bayan sun dakile yunkurin sace mutane a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun dakile yunkurin 'yan bindigan ne na sace mazauna kauyen Gidan Bawa da ke gundumar Kandarawa, karamar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng