Dubu Ta Cika: An Cafke Likita, Lauya da Masu ba 'Yan Bindiga Bayanai
- Askarawan Zamfara sun gabatar da mutane tara da aka kama bisa zargin kasancewa ’yan bindiga, masu leƙen asiri da masu samar da kayan aiki
- Wani matashi mai shekaru 20 ya amsa cewa ya shafe watanni a sansanin fitaccen ɗan bindiga Kachalla Gwaska, inda ya shiga ayyuka a jihohi da ƙasashe daban-daban
- Rundunar ta ce sama da Naira miliyan 226 aka karɓa a matsayin kuɗin fansa daga sace-sacen da ake zargin waɗanda aka kama sun gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Gusau, Zamfara - Askarawan Zamfara, wato Community Protection Guards (CPG), sun gabatar da mutane tara da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.
Daga cikin mutanen da Askawaran suka cafke ciki har da ’yan bindiga, masu ba su bayanan sirri da masu samar musu da kayayyakin aiki.

Source: Facebook
Kwamandan CPG, ritaya AIG Shehu Dalijan, ne ya bayyana hakan a lokacin da aka gabatar da waɗanda ake zargin a Gusau ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2026., cewar rahoton jaridar Vanguard.
Daga cikin waɗanda jami'an rundunar suka kama har da wani da ake zargi da yin aikin lauya ba tare da izini ba.
An ce kama waɗannan mutane ya biyo bayan wasu samamen da rundunar ta gudanar bisa bayanan sirri a sassa daban-daban na Jihar Zamfara.
Matashi ya je sansanin ’yan bindiga
Dalijan ya ce nasarar da rundunar ta samu ta samo asali ne daga bayanan sirri da kuma cikakkun bayanan da wasu mutanen da suka shiga sansanonin miyagun laifuka suka bayar.
Daga cikin waɗanda aka gabatar akwai Abubakar Malan Ori, mai shekaru 20, wanda ya amsa cewa ya shafe watanni yana zama a sansanin fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Gwaska.
Abubakar Malan Ori ya ce ya shiga ayyukan ’yan bindiga a jihohin Zamfara, Kaduna da Niger, da kuma Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, sama da Naira miliyan 226 aka karɓa a matsayin kuɗin fansa daga mutane da dama da aka yi garkuwa da su.
An kama waɗanda ake zargi da satar shanu
Sauran waɗanda aka gabatar sun haɗa da Mamman Haruna da Aliyu Lawali.
An ce mutanen biyu sun bayyana yadda suka shiga manyan ayyukan satar shanu da kai hare-hare tare da wasu fitattun shugabannin ’yan bindiga.
Rundunar ta ce bayanan da waɗanda ake zargin suka bayar sun taimaka wajen fahimtar yadda ƙungiyoyin ’yan bindiga ke gudanar da ayyukansu da kuma mutanen da ke taimaka musu.
An kama likitan ’yan bindiga
A wani babban mataki da CPG ta ce ya yi wa tsarin ayyukan ’yan bindiga illa, rundunar ta kama wani likita da ake zargi da kula da ’yan bindigar da suka samu raunuka.
Ana zargin wanda ake kira Ibrahim Mafindi Titus da yi wa ’yan bindiga magani, tare da amfani da wasu kayan aikin likita da ake samo su daga ƙasashen waje.
Rundunar ta ce kama shi ya kasance babban gibi ga hanyar da ake amfani da ita wajen kula da ’yan bindigar da suka jikkata yayin hare-hare.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta hango matsala, Ribadu ya yi gargadi kan barazanar tsaro a wasu wurare
Sauran waɗanda aka kama
Sauran waɗanda aka gabatar sun haɗa da mutanen da ake zargi da leƙen asiri, masu samar da kayan aiki da ababen hawa, da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, rundunar ta kama wani mai suna Mustapha Muhammed, wanda ake zargi da yin sojan gona.
Ana zargin Muhammed da karɓar kuɗi daga wani ɗan uwan mutumin da ake tsare da shi, bayan ya yi amfani da matsayi na ƙarya a wajen hedikwatar Askarawan Zamfara.

Source: Original
'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta samu gagarumar nasarar kashe 'yan bindiga 17.
Rundunar 'yan sandan ta samu nasarar ne a wani samame da ta kai bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua.
Asali: Legit.ng

