An Kama Dalolin Bogi na Naira Miliyan 30 ana Kokarin Shiga da Su Jama'a

An Kama Dalolin Bogi na Naira Miliyan 30 ana Kokarin Shiga da Su Jama'a

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sami nasarar ƙwato dalolin Amurka na bogi, makamai da aka ƙera a gida guda tara, da kuma motoci biyu da aka sace
  • Jami'an tsaro sun kuma kama mutane uku da ake zargi da ƙoƙarin sayar da wata mota ƙirar GMK ta N70m akan N4m bayan sun shirya sayar da sassan ta
  • Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana haka a madadin kwamishinan ƴan sandan jihar, inda ya nanata aniyar ma'aikatarsu ta dakile masu laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta sami manyan nasarori daban-daban inda ta ƙwato dalolin bogi, makamai, da kuma motoci biyu da aka sace daga wurare daban-daban a cikin jihar.

Sakamakon samun bayanai na sirri, jami'an tsaro sun samu nasarar tauye wa tsagerun daji 'yancin gudanar da ayyukansu na laifi domin samar da yanayi mai kyau ga manoma da sauran mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan tsaro ya yi zarge zarge kan El Rufa'i da ke tsare

Dalolin bogi da aka kama a Kaduna
Wani bangare da tarin dalolin bogi da aka kama a jihar Kaduna. Hoto: Mansur Hassan
Source: Facebook

Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Facebook a ranar Alhamis

An kama barayin daji a Kaduna

DSP Mansir ya bayyana cewa a ranar 31 ga Agusta, rundunar ta sami labarin cewa tsagerun daji suna matsa wa manoma a yankin Kidandan na ƙamarar Hukumar Giwa.

Jami'an ƴan sanda tare da dakarun sa-kai sun kai ɗauki inda bayan musayar wuta, 'yan bindigar suka gudu daji suka bar bindiga, harsasai guda biyu, da kuma babur guda ɗaya.

Ya rubuta cewa:

"Sakamakon ƙarfin wuta na jami'an tsaro, ɓarayin dajin sun tsere zuwa cikin daji, inda suka yar da bindiga guda ɗaya ta pump-action tare da harsasai biyu da kuma babur guda ɗaya."

Haka zalika, a yankin Maraban Jos, jami'an sun ƙwato makamai guda tara da aka ƙera a gida sakamakon kafa shingen bincike bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

An kama motoci da kudin bogi

A gefe guda kuma, jami'an sun kama mutane uku—Hashiru Ibrahim, Mohammed Ibrahim, da Umar Hassan—a Panteka da ke Kurmin Mashi, Kaduna, suna ƙoƙarin sayar da mota ƙirar GMK ta N70m akan N4m bayan sun fasa ta.

Rahoton Punch ya nuna cewa Hashiru ne ya sato motar daga Abeokuta, Jihar Ogun, inda yake aiki a matsayin direba.

An kuma ƙwato wata mota ƙirar Toyota Hilux da aka sato daga Agadez a Jamhuriyar Nijar tare da kama wanda aka tarar da ita, Abubakar Abdullahi.

Motocin da aka kwato a Kaduna
Wasu daga cikin motocin da 'yan sanda suka kama a Kaduna. Hoto: Mansur Hassan
Source: Facebook

A wani farmakin kuma, an kama Kabir Yusuf a Barnawa, Kaduna, dauke da takardun $100 na bogi guda 332 (kimanin N30m) da kuma takardun N1,000 na ƙarya guda shida.

An kama barayin yara a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan FCT ta sake kama wadanda aka taɓa ɗaurewa a kurkuku, Rose Daniel da Blessing John, kan zarginsu da sace yara a Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda 2 a Katsina

An kama waɗanda ake zargin ne a ranar 27 ga Agusta, 2026 sanye da hijabi, a karamar hukumar kuje da ke FCT yayin da suke ƙoƙarin tserewa da wata yarinya mai suna Ummi Mariam Abdullah.

Sanarwar da kakakin 'yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar ta bayyana cewa an kama su ne bayan wani mazaunin yankin da ya shaida lamarin ya ankarar da hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng