'Yan Bindiga Sun Farmaki Mutane ana Shirin Yin Sallah, an Rasa Rayukan Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Farmaki Mutane ana Shirin Yin Sallah, an Rasa Rayukan Bayin Allah

  • Yan bindiga sun kai hari Girkau da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Sokoto, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata wasu uku
  • Maharan sun iso da yawa a kan babura da misalin ƙarfe 2:15 na rana, suka buɗe wa mazauna garin wuta yayin da suke shirin sallar Azahar
  • ’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da adadin shanu da ba a bayyana ba, yayin da mazauna suka ce hare-haren sun zama ruwan dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - ’Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari ƙauyen Girkau da ke ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da mutane kusan 50 suka mutu a wajen satar mai a Najeriya

'Yan bindigan sun kashe aƙalla mutane biyar tare da jikkata wasu uku a yayin mummunan harin da suka kai a kauyen.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na rana ranar Alhamis, lokacin da maharan suka isa garin da yawa a kan babura, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

'Yan bindiga sun budewa mutane wuta

Bayan isarsu, ’yan bindigar sun buɗe wa jama’a wuta ba kakkautawa, lamarin da ya sanya mazauna garin neman mafaka domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin yankin mai suna Usman Girkau ya ce harin ya faru ne lokacin da jama’a ke shirin gudanar da sallar Azahar.

“Muna shirin sallar Azahar ne lokacin da suka kawo mana hari. Suka fara harbi ba kakkautawa.” In ji shi.

An kashe mutane a wasu kauyuka

Usman ya ce ba Girkau kaɗai harin ya shafa ba, domin an kashe wasu mutane a ƙauyukan Jibga da Dukura.

Ya kuma bayyana cewa wani mutum ya nutse a ruwa yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga hannun ’yan bindigar.

Sai dai wani jami’in tsaro da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutane biyar ne suka rasa rayukansu a harin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

Jami’in ya ce wasu mutane uku sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su Babban Asibitin Tambuwal domin samun magani.

An bayyana sunayen waɗanda aka kashe

Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, ya bayyana sunayen huɗu daga cikin waɗanda aka kashe.

Waɗanda ya ambata su ne Dogo Dan Barkeji, mai shekaru 50; Baban Gida Abdullahi, mai shekaru 28; Abubakar Dan Yaki, mai shekaru 50; da Abubakar Aliyu, mai shekaru 35.

Ya ce mutum na biyar ba a gano sunansa ba, kuma mutumin ɗan ƙauyen Dukura ne wanda ya je Girkau ne domin gudanar da wani aiki.

An bayyana waɗanda suka jikkata da sunayen Jamilu Abubakar, Dahiru Yahaya da Adamu Mohammed.

An yi awon gaba da dabbobi

Jami’in tsaron ya ƙara da cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da adadin shanu da ba a tantance ba yayin harin.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har yanzu ba a yi masa cikakken bayani kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga suna lokacinsu a Arewa, sun ƙaƙaba wa Ƴan Sokoto tarar N40m

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kakaba haraji a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kakaba harajin N40m ga mutanen garin Kebbe da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto.

‘Yan bindigar sun kuma yi barazanar kai hari garin tare da kona kadarori idan al’ummar ba ta biya kuɗin da suka nema ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng