2027: An Samu Gwamna na Farko da Ya Goyi bayan Tsarin Atiku na Rage Tsadar Fetur a Najeriya
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce bai kamata muhawarar man fetur ta takaita kan cire tallafi ko dawo da shi ba
- Dan takarar shugaban kasa na APM ya bukaci a sake nazarin tsarin kayyade farashin fetur domin ya dace da yanayin tattalin arzikin Najeriya
- Makinde ya ce bai kamata 'yan Najeriya su dauki nauyin gazawar gwamnati wajen tsaron iyakoki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi kira da a sake duba tsarin kayyade farashin man fetur a Najeriya, yana mai cewa bai kamata muhawarar ta takaita kawai kan cire tallafin mai ko dawo da shi ba.
Makinde ya ce kasancewar Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur, ya kamata a binciki ko tsarin da ake amfani da shi wajen kayyade farashin fetur ya dace da hakikanin yanayin tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan
Atiku ya nuna yadda kalaman IPMAN suka 'kunyata' Tinubu kan dawo da tallafin fetur a Najeriya

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata makala mai taken The Business of Governance, wadda aka wallafa a shafinsa na X a matsayin wani bangare na shirin da ya kira "Reset Nigeria".
Hakan dai ya yi kama da shirin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na ADC, wanda ya yi alkawarin dawo da tallafi ta hanyar inganta tace mai a gida don saukaka wa talaka.
Mafitar da Gwamna Makinde ya kawo
A cewar Makinde, dadaddiyar muhawarar da ake yi kan tallafin mai ta kasa magance muhimmin batun yadda ake kayyade farashin man fetur tun daga tushe.
Ya ce:
"Kowace kasa tana kayyade farashin man fetur bisa tsarinta. Abin da 'yan Najeriya suka cancanci sani shi ne tsarin kayyade farashin da ake amfani da shi yanzu da kuma abubuwan da ake la'akari da su wajen tantance kudin da muke biya a gidan mai."
Makinde ya bukaci gaskiya kan abubuwan da ake amfani da su wajen kayyade farashin fetur, ciki har da farashin danyen mai, kudin tace mai, ribar 'yan kasuwa, farashin musayar kudade, sufuri, haraji da sauran kudade.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi kaca kaca da shirin Atiku na bude iyakoki da dawo da tallafin fetur
Ya ce bayyana wadannan bayanai ga jama'a zai taimaka wa 'yan Najeriya su fahimci dalilin farashin da suke biya tare da kwatanta tsarin da ake amfani da shi yanzu da wasu hanyoyin daban.
Makinde ya soki batun hana fitar da mai
Gwamnan ya kuma yi watsi da hujjar cewa dole ne farashin fetur a cikin gida ya kasance mai tsada domin hana fitar da mai zuwa kasashen makwabta.

Source: Getty Images
Makinde ya ce:
"Ya kamata mu kuma yi watsi da hujjar cewa dole 'yan Najeriya su rika biyan karin kudin man fetur kawai domin a kawar da banbancin farashin da ke sa fitar da shi zuw makwabta ya zama mai riba.
"Bai kamata a dora wa 'yan Najeriya nauyin gazawar gwamnati wajen tabbatar da tsaron iyakokinta ba."
Ya ce saboda haka ya kamata a duba manufofin man fetur na kasar fiye da tambayar ko za a ci gaba da cire tallafin mai ko kuma a dawo da shi.
APM ta hango nasarar Makinde
Kun ji cewa jam’iyyar APM ta bayyana gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin ɗan takarar da ta fi so ya jagoranci haɗakar adawa domin kalubalantar Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Matakin jam’iyyar ya zo ne gabanin taron G-100, wata ƙungiyar siyasa da ke fafutukar samar da ɗan takarar adawa guda ɗaya da zai iya kalubalantar Tinubu.
Asali: Legit.ng