Atiku Ya Nuna Yadda Kalaman IPMAN Suka 'Kunyata' Tinubu kan Dawo Tallafin Fetur a Najeriya

Atiku Ya Nuna Yadda Kalaman IPMAN Suka 'Kunyata' Tinubu kan Dawo Tallafin Fetur a Najeriya

  • Atiku Abubakar ya ce kungiyar dillalan mai ta IPMAN ta fahimci manufarsa ta tallafa wa matatun cikin gida domin rage farashin fetur
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce Najeriya ba za ta ci gaba da fitar da danyen mai tana sayo mai mai tsada ba
  • Ya ce abin kunya ne da kungiyar ta fahimci manufarsa, amma Tinubu yaransa suka shafe lokaci suna kokarin rushe ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi maraba da kiran da kungiyar dillalan mai ta IPMAN ta yi na gwamnatin Najeriya ta shiga tsakanin masu tace mai na cikin gida domin rage farashin fetur.

Atiku ya ce kungiyar, ko da yake ta makara, ta fahimci babban ka'idar tattalin arzikin da ke bayan shirinsa na sake sanya makamashi ya kasance mai saukin farashi ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Alhaji Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan hulda da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar.

Atiku ya ce matakin IPMAN yana da muhimmanci saboda mambobinta su ne ke saye, rabawa da sayar da kayayyakin man fetur kullum.

Ya ce hakan ya sa kungiyar ta fahimci irin illar tsadar fetur ga kasuwanci da iyalan 'yan Najeriya fiye da abin da ya bayyana a matsayin farfagandar gwamnati.

Atiku ya nuna IPMAN na tare da tsarinsa

Atiku ya ce:

“IPMAN ta makara, amma ta zo daidai wajen fahimtar gaskiyar lamarin. Kungiyar yanzu tana ganin bai kamata gwamnati ta tsaya gefe tana kallon yadda farashin fetur ke wahalar da 'yan Najeriya ba.
“Ta kuma ce shiga tsakani cikin tsarin tace mai a cikin gida na iya taimakawa wajen saukar da farashi. Wannan shi ne ainihin ka'idar manufa ta da Shugaba Tinubu da tawagarsa suka shafe makonni suna kokarin rushe ta."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027

Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce gwamnatin Tinubu tana kokarin rikita tsarin tallafin man fetur da ake samu daga shigo da mai daga waje.

Atiku ya yi misali da manomin rogo

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi amfani da misali domin bayyana bambanci tsakanin tsohon tsarin tallafin mai da manufarsa.

Ya ce:

“Bambanci tsakanin tallafin shigo da mai da manufar da na gabatar wa 'yan Najeriya kamar bambancin manomi ne da ya girbe rogo, ya sayar da komai cikin araha sannan ya yi tafiya wani wuri domin ya sayo garri mai tsada da iyalansa za su ci."
“A daya bangaren kuma, akwai manomin da ya samar da damar sarrafa rogon nasa a gida, aka maid shi garri don iyalansa su ci."
Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Tinubu a dama da gidan mai a hadu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Atiku ya ce Najeriya na da danyen mai, saboda haka bai dace kasar ta kasa sarrafa albarkatunta a cikin gida yadda ya kamata sannan ta ce wa jama'a tsadar fetur wani bangare ne na gyaran tattalin arziki ba.

Atiku ya sake tabo Shugaba Tinubu

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci fadar shugaban kasa ta yi bayani kan kwace $460,000 da gwamnatin Amurka ta yi daga asusun Bola Tinubu a 1993.

Atiku ya ce Tinubu ya kamata ya yi bayani kan zargin alakarsa da wani binciken gwamnatin tarayyar Amurka kan safarar miyagun kwayoyi da karkatar da kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262