Lambar Ministoci 20 Ta Fito, Hukuma Ta Bincike Su kan Dukiyoyin da Suka Mallaka

Lambar Ministoci 20 Ta Fito, Hukuma Ta Bincike Su kan Dukiyoyin da Suka Mallaka

  • Shugaban CCB Abdullahi Bello ya ce hukumar ta binciki tare da tantance kadarorin ministoci sama da 20 da manyan sakatarori 30
  • Ya ce CCB ta daina takaita ayyukanta ga karɓar fom ɗin bayyana kadarori, inda yanzu take bincike da kuma gurfanar da waɗanda aka samu da laifi
  • Abdullahi Bello ya ce hukumar na iya fara binciken jami’in gwamnati kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa idan ta samu zargi ko bayanan sirri kan kadarorinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban Hukumar Kula da Da’ar ta Ma’aikatan Gwamnati (CCB), Abdullahi Bello, ya ce sun binciki ministoci.

Abdullahi Bello ya ce hukumar ta binciki tare da tantance kadarorin sama da ministoci 20 da manyan sakatarori 30.

Shugaban CCB ya yi magana kan bincikar ministoci
Shugaban hukumar CCB, Abdullahi Bello Hoto: @CCBNigeria
Source: Twitter

Abdullahi Bello ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan yaƙi da cin hanci da rashawa da bin diddigin kadarori.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya juyo kan 'yan siyasa, ya yi masu gargadi mai zafi

Taron wanda Human and Environmental Development Agenda ta shirya tare da haɗin gwiwar Platform to Protect Whistleblowers in Africa, ya mayar da hankali kan hanyoyin ƙarfafa binciken kadarori da yaƙi da rashawa.

CCB ta daina karɓar fom kawai

Abdullahi Bello ya ce CCB ta wuce matakin karɓar fom ɗin bayyana kadarori kawai, inda yanzu take duba bayanan da jami’an gwamnati suka gabatar, gudanar da bincike kan zargin karya ƙa’ida da kuma gurfanar da waɗanda aka samu da laifi.

“Ba mu ƙara gabatar da fom kawai ba. Yanzu muna binciken fom ɗin, muna gudanar da bincike, sannan muna gurfanar da waɗanda suka aikata laifi,” in ji shi.

Ya ce hukumar ta fi mayar da hankali wajen tantance kadarorin manyan jami’an gwamnati.

“Mun tattauna kuma mun tantance kadarorin sama da ministoci 20, manyan sakatarorin 30, hukumomin lafiya 32 da kuma wasu manyan mutane,” in ji shi.

Ana kiran jami’ai domin tantance bayanai

Kara karanta wannan

"Ta wata hanya daban"; Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafin man fetur

Shugaban CCB ya ce hukumar na gayyatar jami’an gwamnati zuwa ofishinta domin gudanar da bincike kai tsaye kan bayanan kadarorin da suka bayyana.

Ya ce da zarar jami’i ya bayyana kadarorinsa a farkon wa’adin mulkinsa, hukumar za ta tantance su, sannan ta sake yin hakan a ƙarshen wa’adin.

“Idan aka samu bambanci tsakanin abin da ke farkon wa’adin da abin da ke ƙarshensa, kuma ba za a iya bayyana bambancin da kuɗin shiga na halal ba, to muna binciken mutum sannan mu gurfanar da shi,” in ji shi.

Ana iya fara bincike kafin ƙarshen wa’adi

Abdullahi Bello ya jaddada cewa CCB ba sai jami’in gwamnati ya kammala wa’adinsa ba kafin ta fara bincike a kansa.

Ya ce idan aka samu zargi ko bayanan sirri da ke nuna yiwuwar aikata laifi, hukumar na da ikon fara bincike nan take.

“Ba yana nufin sai mun jira ka kammala aiki kafin mu bincike ka ba. Idan akwai wani zargi a kanka, za mu iya bincike. Ko kuma idan muka samu bayanan sirri a kanka, za mu iya bincike,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Za a iya cikin kwanaki 7"; Iran ta sanar da Amurka sharadin bude mashigar Hormuz

CCB ta binciki ministoci
Shugaban CCB na jagorantar wani taro Hoto: @CCBNigeria
Source: Twitter

CCB ta binciki Tunji-Ojo

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar CCB ta aikawa Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, gayyata domin ta yi bincike game da shi.

Ana zargin tsohon kamfanin Ministan ya samu kwangila daga hannun Ministan jin-kai da yaki da talauci watau Betta Edu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng