Hukumar NECO Ta Saki Jarabawar SSCE Ta 2026, Ta Fadi Yawan Daliban da Suka Ci

Hukumar NECO Ta Saki Jarabawar SSCE Ta 2026, Ta Fadi Yawan Daliban da Suka Ci

  • Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar shekarar 2026
  • Alkaluman da NECO ta fitar sun nuna cewa dalibai 804,948 sun ci darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi a jarabawar bana
  • NECO ta ce kashi 84.70 na daliban da suka zana jarabawar sun ci darussa biyar ko fiye da haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Shirya Jarabawa kammala sakandire ta Ƙasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar SSCE ta shekarar 2026.

Hukumar NECO ta bayyana cewa dalibai 804,948, wato kashi 58.67, sun samu maki mai kyau a darussa biyar ko fiye ciki har da Turanci da Lissafi.

Neco.
Tambarin hukumar shirya jarabawar kammala makarantun sakandire ta Najeriya (NECO) Hoto: @neconigeria
Source: UGC

An saki sakamakon jarabawar NECO

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an fitar da sakamakon jarabawar ne kwanaki 63 bayan kammala rubuta jarabawar a fadin makarantun sakandiren Najeriya.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda manyan Najeriya da iyalansu 61 suka saye kadarorin $270m a Amurka

Shugaban hukumar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ne ya sanar da sakin sakamakon a yau Alhamis, 24 ga watan Satumba, 2026.

Ya ce ɗalibai 1,378,048 ne suka yi rajistar jarabawar, yayin da 1,371,992 suka zauna domin rubuta ta. Jarabawar ta fara ne a ranar 15 ga Yuni kuma ta ƙare a ranar 23 ga Yuli, 2026.

Yadda dalibai suka ci jarabawar NECO

A cewar Wushishi, dalibai 1,162,118, wato kashi 84.70, sun samu nasarar cin darussa biyar ko fiye ba tare da la’akari da yadda suka ci a darussan Turanci da Lissafi ba.

Wannan ya bambanta da adadin daliban da suka samu nasara a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, wanda ya kai adadin 804,948, wato kashi 58.67.

An samu raguwar satar amsa

Shugaban NECO ya kuma bayyana cewa an samu gagarumar raguwar satar amsa a jarabawar bana.

Ya ce dalibai 1,406 ne aka samu da hannu a nau’o’in satar amsa daban-daban a shekarar 2026, inda ya ragu sosai idan aka kwatanta da 3,878 da aka samu a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Rigima sabuwa: An maka INEC kara kotu kan zaben 2027

A cewarsa, hakan na nufin an samu raguwar satar amsa da kashi 64.74 idan aka kwatanta da wanda aka samu bara, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Dalibai.
Wasu dalibai suna tsakiyar zana jarabawar NECO a Najeriya Hoto: @neconigeria
Source: Twitter

Wushishi ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu saboda sake naɗa shi a karo na biyu a matsayin shugaban NECO, sannan ya yaba wa Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, saboda amincewarsa da jagorancinsa.

Ya kuma yaba wa hukumomin tsaro, musamman Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), saboda sanya ido a wuraren jarabawar da kuma goyon bayan da suka bayar yayin gudanar da jarabawar.

An dakatar da karin kudin WAEC da NECO

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin karin kudin rajistar jarabawar kammala sakandire ta WAEC da NECO a shekarar 2027.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne domin bai wa masu ruwa da tsaki damar fadar ra'ayoyinsu kafin yanke hukuncin karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262