Sheikh Gumi Ya Yi Barazana ga Masu Alakanta Shi da Goyon bayan 'Yan Bindiga
- Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya musanta cewa yana goyon bayan ’yan bindiga da ke ka'addanci a kasar
- Fitaccen malamin ya bayyana cewa kawai wasu kungiyoyi da mutane da ke juyar da kalamansa da gangan saboda wata bukatar kashin kansu
- Ahmad Gumi ya kara da cewa daga yanzu ba zai bar lamarin haka ba, zai dauki mataki domin a bi masa hakkinsa a kan wadannan zarge-zarge
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa na cewa yana goyon bayan ’yan bindiga ko kare ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Bajimin malamin ya bayyana haka ne a matsayin martani ga masu ikirarin cewa yana nuna goyon baya ga 'yan ta'adda tare da neman a yi sulhu da su.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya bayyana cewa wasu mutane da kungiyoyi masu son tayar da fitina suna juyar da kalamansa da hirarrakinsa domin bata masa suna.
Zargin goyon bayan 'yan bindiga ya fusata Ahmad Gumi
A sanarwar da ya fitar, Malamin ya ce ana amfani da wasu gajerun bidiyo, rubuce-rubuce da sakonni da aka sauya ma’anarsa domin jan hankalin masu kallo a shafukan sada zumunta ba tare da la’akari da wahalhalun da jama’a ke ciki ba.
Malamin ya ce:
“Na lura ana karkatar da wasu daga cikin hirarrakina da hudubobi na dangane da yadda za a magance matsalar ’yan bindiga a Najeriya. Wasu kungiyoyi masu ra’ayin kabilanci, mutane masu son zuciya da kuma masu yada labarai na bangaranci ne ke yin hakan domin neman masu kallo ta hanyar amfani da kanun labarai masu tada hankali.”
Gumi ya jaddada cewa duk wani sako ko bidiyo da ake danganta masa da goyon bayan ’yan bindiga ko kare ayyukansu karya ne tsagwaronta.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ina bayyana karara cewa duk wani bidiyo ko rubutu da ake danganta mani kai tsaye ko a fakaice wanda ke nuna ina goyon bayan ’yan bindiga ko kare ayyukansu bai fito daga gare ni ba.”
Sheikh Gumi zai fara daukan matakin shari'a
Sheikh Gumi ya bayyana kansa a matsayin dan kasa mai biyayya ga Najeriya, yana mai cewa har yanzu yana da yakinin cewa kasar na da babbar damar ci gaba fiye da yadda ake tunani.
Ya bukaci gwamnati, kafafen yada labarai da kuma jama’a su yi watsi da duk wasu bayanai da aka kirkira ko aka sauya domin bata masa suna.
A cewarsa:
“Ina kira ga jama’a, kafafen yada labarai da gwamnatin Najeriya da su yi watsi da wadannan karya da aka kirkira da ake yadawa. Duk wanda ya ci gaba da yada irin wadannan karairayi daga yau zai fuskanci matakin shari’a.”
Malamin ya kuma bayyana fatan cewa Najeriya za ta samu waraka daga matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Kara karanta wannan
FBI ta gano yadda matasa suka hadu, aka kitsa mummunan hari kan masallaci a Amurka
An nemi a kama Ahmad Gumi
A baya, kun ji cewa lauya mai rajin kare hakkin bil’adama, Deji Adeyanju ya bukaci gwamnatin tarayya ta kama Sheikh Ahmad Abubakar Gumi kan kalaman da ya yi kan matsalar tsaron kasar nan.
Mai fafautukar kare hakkin bil adaman ya ce duk wanda ke nuna goyon baya ko tausaya wa ‘yan ta’adda ya kamata a dauke shi tamkar dan ta’adda saboda munin halin da ayyukan yan bindigan ke jefa jama'a.
Gumi ya bayyana a wani bidiyo cewa Fulani makiyaya wani bangare ne na al’umma, yana mai cewa dole Najeriya ta koyi zama tare da su duk da zargin da ake yi na cewa suna da kaso mai tsoka a garkuwa da mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
