Bayan Ƙalubalantar Shi kan Gina Jami'a a Arewa, Atiku Ya Ce ba domin Riba Ya Yi ba
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kare matakin kafa ce Jami’ar AUN ta Amurka da ke Yola a jihar Adamawa
- Atiku ya bayyana cewa da yana neman riba, da ya kafa jami’ar a Abuja ko Lagos, amma ya zaɓi Yola domin tallafa wa al’ummarsa
- Ya kuma ce AUN ba mallakarsa ko iyalinsa ba ce, bayan ya rattaba hannu kan takardar kyauta da ta mayar da jami’ar mallakar al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kare matakin kafa Jami’ar AUN ta Amurka bayan ƙalubalantar shi
Dan takarar shugaban kasa a ADC ya ce ya gina jami'ar ce a Yola a jihar Adamawa domin ci gaban Arewa.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani ga wani mai amfani.
Musabbabin Atiku na kafa jami'ar AUN
Ya ce jami’ar an kafa ta ne domin saka jari a fannin ilimi da ci gaban Arewa, ba wai don samun ribar kansa ba.
A cikin saƙon, ya bayyana irin gudummawar da ya bayar wajen inganta ilimi da kuma shirye-shiryen taimaka wa yara marasa galihu a yankin.
A cewarsa, da neman riba ne babban abin da yake nema, da ya kafa jami’ar a biranen da suka fi samun damar kasuwanci.
Ya ce hakan ya haɗa da Abuja ko Lagos, maimakon ya kafa ta a Yola, inda yake ganin buƙatar ilimi ta fi yawa.
Ya ce:
"Na zaɓi Yola ne saboda ina son saka jari ga mutanena, samar da damammaki, da kuma kawo ingantaccen ilimi kusa da yankin, wannan yanki ya daɗe yana buƙatar ƙarin damar samun ilimi da ci gaba."

Source: Facebook
Matsayar jami'ar AUN ga Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa jami'ar AUN ba ta zama mallakarsa ko ta iyalinsa ba, bayan ya ɗauki mataki.
Ya ce ya rattaba hannu kan takardar kyauta da ta mayar da mallakar jami’ar ga al’umma, domin ta kasance tasu gaba ɗaya.
“Kamar yadda na bayyana a baya, wannan jami’a ba mallakina ba ce, kuma ba mallakar iyalina ba ce.
“Na riga na rattaba hannu kan takardar kyauta da ta mayar da ita ga al’umma. AUN mallakar al’ummar da aka kafa ta domin yi wa hidima ce."
- Atiku Abubakar
Atiku ya kuma yi magana kan wasu shirye-shiryen da aka kafa ta AUN domin taimaka wa yara masu rauni da ke buƙatar tallafi.
A cewarsa, yaran sun koyi karatu ne ta hanyar shirye-shiryen ilimi da ake watsawa ta gidajen rediyo domin isa gare su.
Ya kuma tuna da taimakon da AUN ta bayar bayan sace ɗaliban mata na makarantar Chibok a shekarar 2014.
Atiku ya ce jami’ar ta bai wa wasu matasan mata da suka tsere daga hannun Boko Haram guraben karatu.
Atiku ya ƙaryata cewa zai haramta biyan haya
A wani labarin, an ji cewa twagar yaɗa labaran Atiku Abubakar ta yi martani kan labarin da ke cewa ya yi alkawarin soke biyan kudin haya.
Wani rubutu a X ya wallafa hoton shafin farko na wata jarida, yana zargin Atiku da yin alkawarin ɗaure masu gidaje shekaru 10.
Abdul Rasheeth, mai taimaka wa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, ya bukaci jama’a su yi watsi da labarin tare da dogaro da hanyoyin sadarwar Atiku.
Asali: Legit.ng


