Tinubu Ya Fadi Halayen Shettima na Gari da Ya Cika Shekara 60 da Haihuwa
- Shugaba Bola Tinubu ya taya mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa
- Tinubu ya yaba da tarihin Shettima a harkar banki da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen yi wa Borno da Najeriya hidima a matsayinsa na gwamna
- Shugaban ya ce biyayya, hikima da kishin Shettima ga nasarar Renewed Hope sun kasance muhimman abubuwan da suka taimaka wa gwamnatinsu a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya mataimakinsa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa kuma abokin hulɗa amintacce.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026, inda ya ce Shettima ba kawai abokin aiki ba ne, har ila yau mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Tinubu ya taya matar Shettima, Nana, ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasarsa murnar wannan rana mai tarihi.
Tinubu ya yaba wa Shettima
Tinubu ya ce yana murnar zagayowar ranar haihuwar Shettima tare da iyalansa, yana mai bayyana shi a matsayin mutum mai kishin ƙasa da aka gina rayuwarsa kan hidima, jajircewa da sadaukarwa.
Punch ta rahoto cewa ya ce:
“Kashim ɗan kishin ƙasa ne wanda rayuwarsa ta kasance cike da hidima, jajircewa da sadaukarwa ga kyawawan manufofi.”
Shugaban ya kuma yaba da tarihin Shettima a fannin banki da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen yi wa Borno da Najeriya hidima.
Batun biyayyar Shettima ga APC
Shugaban ya kuma yaba da biyayyar Shettima ga APC, da goyon bayan da yake bai wa gwamnatinsa da kuma jajircewarsa wajen ganin an cimma manufofin Renewed Hope Agenda.
Tinubu ya ce a matsayinsa na shugaban NEC, Shettima ya samar da jagoranci mai ma’ana wajen daidaita manufofin tattalin arziki da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

Kara karanta wannan
Kano da wasu jihohi 19 sun fito a wuraren da Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027
Ya ƙara da cewa mutunta kundin tsarin mulki, cibiyoyin dimokuraɗiyya, tattaunawa da neman shawarwari da Shettima yake yi sun taimaka wajen ƙarfafa shugabanci na gari.

Source: Facebook
Tinubu ya gode wa Shettima
Shugaban ya ce biyayyar Shettima, hikimarsa da kishin aikinsa sun kasance muhimman abubuwa ga gwamnatin da yake jagoranta.
Ya ce:
“Dole ne in gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima saboda goyon bayansa da haɗin gwiwarsa yayin da muke ci gaba da haɗa hannu wajen cika alkawuran Renewed Hope ga ’yan Najeriya.”
Abin da Shettima ya nema
A wani labarin, mun ruwaito cewa Kashim Shettima ya roƙi 'yan uwa da abokai da su guji ba shi kyaututtuka ko shirya masa bukukuwa masu tsada yayin da yake cika shekaru 60.
Shettima ya bukaci abokansa da magoya bayansa su karkatar da duk wani kuɗin da za su kashe wajen yi masa kyauta ko biki zuwa ayyukan agaji da sauran abubuwan da za su amfani al’umma.
Ya ce ya sha roƙon abokansa da magoya bayansa da kada su kashe kuɗi wajen sayen masa kyaututtuka ko gudanar da wani abu mai tsadar gaske saboda ranar haihuwarsa.
Asali: Legit.ng
